ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

2027: Wajibi Ne A Saka Sakamakon Zaɓe A Na’ura – Farfesa Jega

by Leadership Hausa
6 months ago
Zaɓe

Tsohon Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta (INEC), Farfesa Attahiru Jega, ya yi kira a yi gyaran dokokin da suka dace na dokar zabe ta 2022, domin sanya sakamakon zabe ta na’ura ya zama wajibi a zabe mai zuwa.

Da yake gabatar da takardar mai taken, ‘Bukatar kawo sauyi domin karfafa cibiyoyin dimokuradiyya a Nijeriya’, wanda kungiyar ‘The Cobenant Nation Global’ ta shirya a Lagos, Jega ya nemi a kara amfani da fasahar zamani a zabe domin inganta shugabanci.

  • Dalilin Da Ya Sa Tinubu Ya Nada Jega A Matsayin Mai Ba Shi Shawara Kan Samar Da Sauyin Noma Da Kiwo
  • Tinubu Ya Naɗa Jega Muƙamin Mai Ba Shi Shawara Kan Harkar Kiwo

Idan za a iya tunawa dai, an sami cece-kuce game da batun watsawa sakamakon zabe ta na’ura a zaben 2023, wanda dimbin ‘yan Nijeriya suka yi shakku kan sakamakon zaben shugaban kasa.

ADVERTISEMENT

Jega ya kasance farfesa na kimiyyar siyasa, ya bayyana cewa dole ne a warware rashin fahimtar da ta shafi aika sakamakon zabe ta na’ura.

“Misali, cire rashin fahimta a sashe na 64 na dokar zabe ta 2022, dangane da matakan da ake bi na jinkirta sakamakon zabe a na’urai. A sake duba hanyoyin nada shugaban INEC da kwamishinonin zabe na jihohi, a cire ko kuma a rage tasirin bangaren zantarwa wajen karfin kula da ‘yancin hukumar zabe,” in ji shi.

LABARAI MASU NASABA

Cikin Sauƙi Na Yanke Shawarar Komawa APC – Gwamna Fubara

Ba Zan Taɓa Komawa Jam’iyyar APC Ba — Abaribe

Batun sauya sheka da ke faruwa a cikin tsarin siyasar Nijeriya, Jega ya kira a hana sauya sheka ga wadanda aka zaba a bangaren zantarwa da kuma ‘yan majalisa.

Ya kuma yi kira ga jami’an INEC a matakin tarayya, da na jihohi su shirya gudanar da zaben cike gurbi da zarar an samu labari game da sauya sheka.

Ya ba da shawarar cewa ‘yan Nijeriya da ke zaune a kasashen waje su dunga kada kuri’a a zaben shugaban kasa, kuma ya yi kira a tsaurara dokoki kan kudaden kamfen ciki har samar da hukumar da za ta sa ido kan aiwatar da hukunci.

Jega ya yi nadama da cewa daya daga cikin manyan kalubalen da Nijeriya take fuskanta shi ne, yadda za a iya hana mulkin kama-karya, ” a cikin yanayin dimokuradiyya, tun daga shekarar 1999, lokacin da muka fara sauyi daga mulkin soja zuwa mulkin dimokuradiyya na farar hula.”

Ya ce, ‘Mun dauka ta hanyar dimokuradiyya kasarmu za ta samun ci gaba mai ma’ana da kyakkyawan shugabanci, amma sai dai lamarin ba haka yake ba.

“Abin takaici shi ne, bayan tsawon lokaci a cikin mulkin dimokuradiyya, maimakon karfafa dimokuradiyya, amma kuma an samu mulkin kama-karya a kasarmu kamar ba mulkin dimokuradiyya muke yi ba.”

 

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Siyasa

Cikin Sauƙi Na Yanke Shawarar Komawa APC – Gwamna Fubara

December 18, 2025
Ba Zan Taɓa Komawa Jam’iyyar APC Ba — Abaribe
Siyasa

Ba Zan Taɓa Komawa Jam’iyyar APC Ba — Abaribe

December 16, 2025
El-Rufai Ya Ƙaryata Rahoton Goyon Bayan Yanki Ko Wani Mutum A Zaɓen 2027
Siyasa

El-Rufai Ya Ƙaryata Rahoton Goyon Bayan Yanki Ko Wani Mutum A Zaɓen 2027

December 15, 2025
Next Post
Gwamnan Abba Kabir Yusuf tare da Arch. Ali Hassan

Abba Ya Dace Ya Zama Gwamnan Kano Na Har Abada Ba Shekaru 8 Kaɗai Ba - Arch Ali Hassan

LABARAI MASU NASABA

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

December 21, 2025
Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

December 21, 2025
Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

December 21, 2025
Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

December 21, 2025
An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

December 21, 2025
Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

December 21, 2025
Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

December 21, 2025
Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.