A ranar 30 ga watan Oktoba na shekarar 2023, dan wasa Lionel Messi ya lashe kyutar gwarzon dan kwallon kafa na duniya na 2023, wato Ballon d’Or karo na takwas jimilla.
Messi tsohon dan wasan Barcelona da Paris St Germain mai buga wasa a Inter Miami a Amurka ya dauki kofin duniya a Katar a 2022, kofin da ya daukar wa Argentina na uku a tarihi. Messi, shi ne ya ja ragamar Argentina ta lashe babban kofin duniya na farko a wajensa, kuma na uku a kasar jimilla, sannan Aitana Bonmati ce ta zama gwarzuwar kwallon kafa ta 2023, wato macen da ta lashe Ballon d’Or.
- Ci Gaba Da Gudanar Da Sha’Anin Da Mao Zedong Ya Kaddamar, Shi Ne Abu Mafi Dacewa Game Da Tunawa Da Shi
- NAF Ta Lalata Haramtattun Wuraren Tace Mai Guda 6 A Ribas
Bonmati, mai shekara 25, ta dauki Champions League da kofin Sifaniya a Barcelona a bara – da lashe kofin duniya a bana tare da tawagar Sifaniya. Sai Sam Kerr ta Chelsea da Australia ce ta biyu, sai ‘yar kwallon Barcelona da tawagar Sifaniya, Salma Paralluelo ce ta uku.
Karo na takwas kenan da Messi ke lashe kyautar ta Ballon d’Or, bayan da ya dauka a 2009, 2010, 2011, 2012, 2015, 2019 da kuma 2021 sai dai ya lashe kyautar 2021 tare da Robert Lewandowski, ya kuma yi wa Cristiano Ronaldo tazara mai biyar da ya ci a 2008, 2013, 2014, 2016 da kuma 2017).
Masu uku-uku a tarihin karbar kyautar Ballon d”Or sun hada da Michel Platini da Marco ban Basten da kuma Johan Cruyff sai Karim Benzema wanda ya lashe kyautar a bara lokacin yana buga wasa a Real Madrid, a kakar da Messi bai kai bantensa ba cikin ‘yan takara.
Wasu na ganin Erling Haaland ne ya kamata ya lashe Ballon d’Or na bana, bayan da ya ci Champions League da Premier League da FA Cup a Manchester City a bara, sannan Haalan, tsohon dan wasan Borussia Dortmund ya ci kwallo 52 a wasann 53 a kakar da ta wuce.
Wasu da suka lashe kyautuka:
Haaland ya karbi kyautar Gerd Muller – kyauta ce saboda zun-zurutun kwallaye 52 da ya zura a raga a wasa 53 a kakar da ta wuce.
Bellingham ya lashe kyautar Kopa Trophy – kyauta ce ta matashin da ba kamarsa a duniya a 2023.
Binicius Jr, ya karbi kyautar Socrates – Dan kasar Brazil ya samu wannan lambar yabon sakamakon gidauniyarsa ta taimakawa yara marasa gata a kasarsa.
Emiliano Martinez ya lashe kyautar Yashin – Tsohon wanda ya buga wasan aro a Odford United, shi ne gwarzon mai tsaron raga a 2023. Manchester City ce kungiyar kwallon kafa ta maza da ba kamarta a bara. Kungiyar ta lashe kofin Champions League da Premier League da FA Cup a bara, sannan tana da ‘yan wasa bakwai daga 30 da suka yi takarar kyautar Ballon d’Or.
Kungiyar Barcelona ta mata ce kan gaba a bajinta a bana. Ta lashe Champions League a bara da kofin Sifaniya ‘yan wasanta shida suna cikin takarar Ballon d’Or bangaren mata.
Manchester City Ta Karya Tarihin United
Har ila yau, a ranar 22 ga watan Disamba na wannan shekarar kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta kammala lashe kofuna biyar bayan da tun farko ta kammala kakar wasan bana da kofuna uku a cikin jakarta inda ta lashe gasar firimiya da kofin kalubale da daukar kofin zakarun turai bayan ta doke Inter Milan da ci 1-0 a wasan karshe.
Wasan karshen da suka fafata da Inter Millan, sun buga wasan ne a filin Olympic na Atuturk da ke Istanbul a kasar Turkiyya inda dan wasa Rodri ya zura kwallon a raga.
Tun a watan Mayu kungiyar ta lashe kofuna biyu – na Gasar Firimiya ta Ingila da Gasar FA, kuma hakan na nufin ta zama kungiyar Turai ta biyu da ta lashe kofuna uku a kakar wasa daya – Manchester United ta kafa wannan tarihi a 1999.
Kazalika wannan bajinta ta Pep Guardiola ya jaddada matsayinsa na zama daya daga cikin koci mafi shahara inda ya ci kofinsa na uku na Zakarun Turai bayan ya lashe biyu a Barcelona, na karshe shi ne wanda ya dauka a 2011.
‘Yan wasan na Guardiola sun yi gumurzu sosai da ‘yan wasan Inter Milan, wadanda suka nuna matukar hazaka, sai dai a minti na 68 Rodri ya zura kwallon da ta ba su nasara.
Manchester City ta yi nasara ne duk da cewa zakakurin dan wasan tsakiyarta Kebin De Bruyne ya ji rauni kafin a tafi hutun rabin lokaci lamarin da ya sa aka cire shi daga wasan.
Spain Ta Lashe Gasar Cin Kofin Duniya
A ranar 20 ga watan Agusta na wannan shekarar ta 2023 kasar Spain ta lallasa Ingila a wasan karshe na cin kofin kwallon kafa na duniya na mata inda ta lashe kofin a karon farko a tarihi. Kwallon da ’yar wasa Olga Carmona ta ci a minti na 29 ce dai ta bai wa Sifaniya nasarar a wasan da aka fafata kuma an buga wasan ne a Sydney, Babban Birnin Kasar Austaraliya.
Tawagar ta kasar Sifaniya dai ta rike wuta ne tun daga farkon wasan, inda duk yunkurin da matan na Ingila suka yi na farke kwallon ya ci tura har aka tashi wasan.
’Yar wasan nan ta Sifaniya da ta taba lashe kambun Ballon d’Or ta duniya, Aledia Putellas dai an ajiye ta daga jerin ’yan wasan da suka buga wa kasarta wasan na karshe da Ingila.
‘Yan Wasan Da Suka Saudiya Daga Turai
Tun bayan komawar fitaccen dan wasan kwallon kafa Cristiano Ronaldo kasar Saudiyya da buga wasa bayan ya raba gari da kungiyar Manchester United, sai gasar kasar ta kara armashi a idon masoya kwallo.
A wannan shekarar an samu kwararar ‘yan wasa da dama daga turai zuwa kasar ta Saudiyya, wasu daga cikin ‘yan wasan ma babu wanda ya yi tunanin cewa za su dauki matakin canja sheka zuwa kasar ta Saudiyya saboda ana ganin akwai sauran lokaci.
Sai dai a daidai lokacin da za a fara kakar bana, kungiyoyin kasar sun rikita kasuwar hada-hadar ’yan wasa, inda suka yi ta taya manyan fitattun ’yan wasan duniya da kudi mai yawa kuma suka dinga tafiya.
Dan wasan kasar Senegal Koulibaly ya bayyana cewa saboda kasancewar yana bukatar kudi sosai da zai ci gaba da daukar dawaniniyar iyalansa da ’yan uwansa da kuma wasu ayyuka da yake so ya yi a kauyen da ya fito, da kuma kasancewarsa Musulmi ne suka sa ya yanke shawarar komawa Saudiyya da buga kwallo.
Wani abu da ya tayar da kura shi ne yadda dan wasa Cristiano Ronaldo ya yi Sujjada bayan zura kwallo a wani wasa a kasar, inda aka rika yada hoton Sujjadar ana bayanai a kai
Karim Benzema: Daga Real Madrid zuwa Al Ittihad Karim Benzema, wanda shi ne Gwarzon dan kwallon duniya na yanzu ya bar kungiyar Real Madrid ta Sifaniya duk da cewa sun bukaci ya kara sanya hannu a kwantaragi domin ci gaba da zama kungiyar inda ya koma Al Ittihad ta Saudiyya.
Barin Real Madrid ya yi matukar zuwa wa magoya bayan kungiyar da ba-zata, kasancewar shi ne Kyaftin, sannan ba a samu shakku ba a kan kasancewarsa wanda yake jan ragamar kungiyar, ballanta a fara tunanin ajiye shi a benci. Ya koma kungiyar Al Ittihad ce wadda ta lashe Gasar Firimiyar Saudiyya ta bara, inda ya sanya hannu a kwantaragin shekara uku a kan Fam miliyan 107 duk shekara, kudin da suka ninka kudin da yake samu a Real Madrid.
Da yake bayani a lokacin gabatar da shi ga magoya bayan kungiyar, Karim farawa ya yi da sallama, sannan ya ce a matsayinsa na Musulmi ya ji dadin komawa Saudiyya da buga wasa, sannan ya ce kasancewar Cristiano Ronaldo, wanda ya bayyana a matsayin abokinsa a gasar kasar ya sa ya samu saukin yanke shawarar.