• English
  • Business News
Saturday, August 23, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Rayuwar ‘Yan Arewa Na Cikin Hadari, Yayin Da Gurbataccen Gishiri Ya Fantsama A Kasuwanni

by Rabi'u Ali Indabawa
4 months ago
in Labarai
0
Rayuwar ‘Yan Arewa Na Cikin Hadari, Yayin Da Gurbataccen Gishiri Ya Fantsama A Kasuwanni
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Wata ziyara da aka kai wasu daga cikin Manyan kasuwannin Arewacin Nijeriya, ya bankado sirrin kwararowar wasu haramtattun sinadaran dandano.

An gudanar da aikin lalata sinadarin dandano na monosodium glutamate (MSG) wadanda bincike ya nuna ba su da wata shaida ta amincewa, kuma aka sake nade su aka mayar da su cikin wasu jakunkunan leda domin ci gaba da sayar da su ga al’umma.

  • Gobara Ta Ƙone Shaguna 12 A Kasuwar Siminti Ta Oyo
  • Ministan Yaɗa Labarai Ya Zayyana Wa Masu Zuba Jari Na Faransa Irin Sauye-sauyen Tattalin Arzikin Nijeriya

Babban abin takaicin shi ne yadda shan wannan haramtaccen sinadari na MSG ke kara yaduwa tsakanin ’yan Arewa wanda hakan ke haifar da babbar illa ga lafiya.

Duk da tashi tsayen da Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta kasa (NAFDAC) ta yi wajen fadakarwa, masu saye da sayar da kayayyaki sun yi kunnen uwar shegu gami da ci gaba da gudanar da harkokin wadannan sinadarai na MSG wajen sake mayar da su cikin mazubi da ci gaba kasuwancinsu.

Ana sayar da wannan sinadari ne kai tsaye saboda bashi da wata alama a jikin mazubin da aka nade shi, sannan masu sayen babu ruwansu da binciken shin ko maganin ingantacce ne ko akasin haka.

Labarai Masu Nasaba

Shirin Ahmed Isa Na Brekete Family: Maslaha Ko Matsala?

Zargin Shan Guba: ’Yan Nijeriya Biyu Sun Mutu A Libya

Ba kamar kayayyakin manyan kamfanoni irin su Ajinomoto, Bedan wadanda aka zuba su a cikin kwali, ana sayar da su cikin lafiyayyen mazubi kuma NAFDAC ta amince da su ba, wadannan danyun kaya ne da ba su da wata alama.

Babban abin ban tsoro shi ne ba za a iya gano masana’antunsu don bincikar sahihancinsu ba. Da alama a yankin Arewacin Nijeriya din ake yin su amma an gaza gano hakan ko kuma an gano amma wa’alla saboda yawan bukatu an kasa dakilewa.

Bincike ya nuna cewa a kasuwar Singer da Abubakar Rimi da ke Kano, ana sayar da buhu mai nauyin kilo giram 25 na wannan sinadari kan Naira 45,000, wanda ke bai wa ‘yan kasuwa damar sayar da su a kanana wurare, ciki har da auna shi da abin da mazauna yankin ke kira ‘mudu’.

A manyan kasuwannin Kaduna da Maiduguri, kasuwar Sabon Gari da ke Sokoto, ana sayar da buhu mai nauyin kilogiram 25 a tsakanin Naira 46,000 zuwa Naira 50,000.

A cikin jaka mai nauyin kilo giram 25, ana iya samun kamar mudu ‘10 zuwa 15 ‘.

Abokan ciniki, ba tare da la’akari da hadarin dake tattare da kiwon lafiya ba, sun fi son wannan haramtaccen samfuri saboda yawan abin da za su samu daga mudu da kuma saukin yin almundahana ta hanyar cakuda shi da gishiri don kara yawansa da samun riba.

A kwanakin baya ne hukumar ta NAFDAC ta rufe wani dakin ajiyar kaya na kamfanin ‘DEE-LITE IMPED Distribution Co. Ltd’ da ke Jihar Sokoto, bayan ta gano wani adadi mai yawa na kayan abinci marasa rajista da suka hada da buhu 5,347 na MSG.

Rumbun ajiyar da ke kan titin Coca-Cola, daura da Western Bypass a Sokoto, an gano ya saba wa ka’idojin hukumar NAFDAC. A cewar hukumar ta NAFDAC, kamfanin ya shigo da haramtaccen samfurin MSG babu izini a karkashin takardar izinin sarrafawa amma an same shi yana sayar da samfurin kai tsaye, wanda haramun ne kuma yana da hadari ga lafiyar dan’Adam.

Wani masani kan harkokin kiwon lafiya da ke zaune a Gombe, Dokta Abdullahi Guruji ya ce ya kamata masu amfani da su su yi hattara da abubuwan da suke amfani da su domin gujewa duk wata matsala a fannin lafiya. Guruji ya ce ya zama wajibi masu amfani da su daina sadaukar da lafiyarsu a kan burin farashin kayan abinci masu arha.

A cewarsa, bai kamata a ce alhakin kare lafiyar mutum ya takaita ga hukumar NAFDAC da SON da sauran hukumomi kadai ba. Ya bukaci kowane dan Nijeriya da ya kula da kansa da kuma sauran ‘yan kasarsa domin kaucewa wannan hatsarin da ke kunno kai a harkar lafiya.

A yayin da yake kira ga masu sayar da abinci da su taka rawar gani a wannan fanni, ya bukace su da su kula da lafiyar kwastomominsu ta hanyar yin amfani da ingantattun kayayyakin dafa abinci.

Sai dai kwarare a fannin lafiyar ya dora wa hukumar ta NAFDAC alhakin kara kaimi a fannin tabbatar da doka da oda inda ya ce yin hakan zai dakile ayyukan marasa kishin Nijeriya da suke jajircewa wajen cutar da ‘yan Nijeriya.

“Duk lokacin da muka ziyarci kasuwa, za mu ceci mutane da yawa daga matsalolin kiwon lafiya ta hanyar rufe shagunan masu sayar da monosodium glutamate, masu sayar da magungunan jabu / marasa inganci, da masu siyar da abubuwan sha masu dandano, na cikin kwalba a cikin sauran abubuwan da ke zama abin sha,” in ji shi.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: ArewaCutaGishiriHadariKasuwanniLafiya
ShareTweetSendShare
Previous Post

Yadda Bankin Stanbic IBTC Ke Bunkasa Tattalin Arzikin Abokan Huldarsa

Next Post

Salah Ya Ƙulla Sabuwar Yarjejeniyar Shekaru 2 Da Liverpool

Related

Shirin Ahmed Isa Na Brekete Family: Maslaha Ko Matsala?
Labarai

Shirin Ahmed Isa Na Brekete Family: Maslaha Ko Matsala?

4 hours ago
Zargin Shan Guba: ’Yan Nijeriya Biyu Sun Mutu A Libya
Kotu Da Ɗansanda

Zargin Shan Guba: ’Yan Nijeriya Biyu Sun Mutu A Libya

5 hours ago
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta
Kotu Da Ɗansanda

Yadda Wani Mai Unguwa Ya Yi Wa ‘Yar Shekara 12 Fyade A Gombe

6 hours ago
NDLEA Ta Kama Matashi Da Tabar Wiwi Ta Naira Miliyan 10 A Kano
Manyan Labarai

NDLEA Ta Kama Matashi Da Tabar Wiwi Ta Naira Miliyan 10 A Kano

7 hours ago
Garkuwa Da Mutane: Wani Ba’indiye Da Ake Zargi Ya Nemi Shafa Wa ‘Yan Nijeriya Kashin Kaji
Kotu Da Ɗansanda

Garkuwa Da Mutane: Wani Ba’indiye Da Ake Zargi Ya Nemi Shafa Wa ‘Yan Nijeriya Kashin Kaji

8 hours ago
Matasa Sun Nemi A Tura Sojoji Don Korar Ƴan Bindiga Daga Kwara
Tsaro

Matasa Sun Nemi A Tura Sojoji Don Korar Ƴan Bindiga Daga Kwara

8 hours ago
Next Post
Salah Ya Ƙulla Sabuwar Yarjejeniyar Shekaru 2 Da Liverpool

Salah Ya Ƙulla Sabuwar Yarjejeniyar Shekaru 2 Da Liverpool

LABARAI MASU NASABA

Taron Kare Hakkin Dan Adam Na Sin Da Afirka Na Farko Ya Nemi Hada Karfi Don Tabbatar Da ‘Yancin Samun Ci Gaba

Taron Kare Hakkin Dan Adam Na Sin Da Afirka Na Farko Ya Nemi Hada Karfi Don Tabbatar Da ‘Yancin Samun Ci Gaba

August 23, 2025
Bangaren Kasuwancin “E-Commerce” Na Kasar Sin Ya Karu Sosai A Watanni 7 Na Farkon Bana

Bangaren Kasuwancin “E-Commerce” Na Kasar Sin Ya Karu Sosai A Watanni 7 Na Farkon Bana

August 23, 2025
Yajin Aiki: Kungiyar ASUP Ta Ba Gwamntin Tarayya Wa’adin Kwana 21 Ta Biya Masu Bukatu

Yajin Aiki: Kungiyar ASUP Ta Ba Gwamntin Tarayya Wa’adin Kwana 21 Ta Biya Masu Bukatu

August 23, 2025
Shirin Ahmed Isa Na Brekete Family: Maslaha Ko Matsala?

Shirin Ahmed Isa Na Brekete Family: Maslaha Ko Matsala?

August 23, 2025
Zargin Shan Guba: ’Yan Nijeriya Biyu Sun Mutu A Libya

Zargin Shan Guba: ’Yan Nijeriya Biyu Sun Mutu A Libya

August 23, 2025
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

Yadda Wani Mai Unguwa Ya Yi Wa ‘Yar Shekara 12 Fyade A Gombe

August 23, 2025
NDLEA Ta Kama Matashi Da Tabar Wiwi Ta Naira Miliyan 10 A Kano

NDLEA Ta Kama Matashi Da Tabar Wiwi Ta Naira Miliyan 10 A Kano

August 23, 2025
Garkuwa Da Mutane: Wani Ba’indiye Da Ake Zargi Ya Nemi Shafa Wa ‘Yan Nijeriya Kashin Kaji

Garkuwa Da Mutane: Wani Ba’indiye Da Ake Zargi Ya Nemi Shafa Wa ‘Yan Nijeriya Kashin Kaji

August 23, 2025
Matasa Sun Nemi A Tura Sojoji Don Korar Ƴan Bindiga Daga Kwara

Matasa Sun Nemi A Tura Sojoji Don Korar Ƴan Bindiga Daga Kwara

August 23, 2025
Hotuna: Shettima Ya Wakilci Shugaba Tinubu Wajen Jana’izar Sarkin Zuru

Hotuna: Shettima Ya Wakilci Shugaba Tinubu Wajen Jana’izar Sarkin Zuru

August 23, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.