• English
  • Business News
Monday, August 25, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ban Dauki Harkar Fim Da Wasa Ba -Hauwa Ayawa 

by Rabi'at Sidi Bala
3 months ago
in Nishadi
0
Ban Dauki Harkar Fim Da Wasa Ba -Hauwa Ayawa 
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Daya daga cikin fitattun jaruman finafinan hausa dake masana’antar kannywood HAUWA ABUBAKAR AYAWA wacce aka fi sani da AZIMA GIDAN BADAMASI jarumar da ta shafe tsahon shekaru a cikin masana’antar kuma ‘ya ga tsohuwar furodusa a cikin masana’antar ta kannywood, shafin Rumbun Nishadi yayi cozali da ita inda ta bayyanawa masu karatu wasu batutuwa da suka shafi sana’arta ta fim har ma da wasu batutuwan da suka shafi rayuwarta.

Wane irin nasarori ki ka samu game da fim?

  • Tsokaci Kan Yadda Wasu Matasa Ke Yin Aure Ba Tare Da Sana’a Ba
  • Dan Asalin Jihar Kano Ya Kafa Tarihin Kirkirar Manhaja Mai Auna Tsayin Bishiya A Faransa

Akwai an samu Alhamdulillah cikin ikon Allah, kin ga babbar ni’ima shi ne mutane suna ganin mutuncinka kuma kana da lafiya shi ne ma babbar ni’ima, Allah ya barka da lafiyarka za ka tashi ka bauta masa cikin ikon Allah, kuma in ka tashi ka juya ka ga baka rasa abubuwa na rayuwa ba sai ka kara gode wa Allah to, muna cikin godiya sai mu roki Allah ya kara ninko mana, kin san in kana cikin rahma kana son Allah ya kara sa maka jin dadi to muna rokon ubangiji Allah ya ninka mana ni’imominsa fiye da wanda ya ba mu yanzu.

Wane abu ne ya taba faruwa da ke cikin masana’antar wanda ba za ki taba iya mantawa da shi ba na farin ciki ko akasin haka?

To, bakin ciki dai babu, na farin ciki kuma akwai sosai wanda in ka tuna kana zaune da kowa lafiya sai ka godewa Allah kai salati ga Annabi, Allah ya kara mana son Annabi, kuma Allah ya kara mana daraja a idon kowa dan alfarmar Annabi Muhammad (S.a.w).

Labarai Masu Nasaba

Babban Burina A Harkar Fim Shi Ne Ganin Habakar Harshe Da Al’adun Hausa—Murtala Abdullah

Na Hadu Da Azzalumai Da Mayaudara Farkon Shigata Kannywood – Dan’duniya

Mene ne burinki na gaba game da fim?

Burina shi ne a ce yau ga ni ni ma na fito da kudina a ce yau ni ce furodusa ta kaina da kaina, ina rokon ubangiji Allah ya nuna mun ranar nan inada wannan burin sosai ace ni zan yi furodusin fim dina da kaina kuma in sha Allahu muna nan muna rokon Allah yayi mana zabin abin da ya fi zama alkhairi, in sha Allah.

Wadanne jarumai ne suke burge ki tun kafin ki fara fim har ma da yanzu da ki ke cikin masana’antar su waye suka zama allon kwaikwayonki?

Zan iya ce miki ‘acting’ din kowa yana burge ni kowa da yanayin aktin din da za ka ga kawai ka yi wani abu ne karamun abu ne wanda ma bai burge wancen ba amma ni ya burge ni, kowa yana burge ni, kuma kowa jarumi na ne kowa na burge ni cikin ikon Allah.

Wane ne ubangidanki a cikin masana’antar kannywood?

Ubangidana babana maganin kuka na, ai ni ubangida na rage masa baba ne, kamar mahaifi na dauke shi, Baba Falalu, Falalu A. Dorayi shi ne komai na a ‘industry’.

Da yawa wasu daga cikin ‘yan kannywood za ki ji suna cewa akwai karancin girmamawa ga na kasa zuwa ga na sama, me za ki ce a kan hakan?

Allah ya shirye mu gabadaya, amma ni dai gaskiya duk wanda ya sanni ya san ina girmama na sama da ni kuma har na kasa da ni, saboda zan iya ce miki ni ko mutum ya girme ni ko da kani gare ni ni ban ma iya kiran sunan shi sai dai in dauki wani abun in laka masa, ko in ce dan’uwa ko na ce yayana na san ka girme ni amma sunan naka ne ba zan iya kira ba, gaskiya ni bana daga cikin wadannan wanda ba sa darajanta na sama gare su, kuma ina fatan ubangiji Allah ya shirye mu gabadaya, saboda in ka darajanta wani kanka ka darajanta shi ne kawai.

Idan aka ce ki fadi abu daya wanda sam bai yi miki ba a cikin masana’antar kannywood wane abu za ki ce?

Abu daya da zan ce shi ne zan iya cewa dan Allah mu kaunaci junanmu gabadaya, mu so junanmu gabadaya

Ya batun aure shin kin taba yin aure ko kuwa tukunna dai, kuma yaushe ki ke saka ran yin aure?

A’a ‘yar’uwa ban taba yin aure ba amma addu’ar mu kenan muna rokon Allah ubangiji ya kawo mana miji nagari wanda in muka shiga mun shiga kenan [Dariya]… mutu-ka-raba, kuma sai a taya mu da addu’a.

Shin za ki iya auren abokin aikinki dan fim, ko kuwa ba ki da irin wannan ra’ayin?

Eh! sosai, wallahi sosai zan iya indai yana sona ina son shi lafiya lau zan aure shi, kuma mu zauna cikin ikon Allah, wallahi zan iya.

Misali a ce kin yi aure kin haifi ‘ya, kuma tana son yin fim shin za ki bar ta ta yi ko kuma ba ki da ra’ayin hakan?

‘Yar’uwa indai nayi aure na haifi ‘ya tana so zan bar ta, ni fa fim sana’a na dauke ta, wallahi sana’a babba na dauke ta, wanda ake ci gaba a cikinsa, ban dauki fim da wasa ba da gaske na dauke shi, saboda na san har da zuciyata ni sana’a na dauke ta kuma sana’a nake to, wallahi wallahi har da zuciyata nake fito miki da maganar wallahi tallahi indai ‘ya ta za ta yi cikin ikon Allah ni zan rika ma kai ta lokeshan din, zan je na kai ta na jira ta ko in je idan ta gama na je na dauko kaya ta karshe kenan.

Wacce shawara za ki bawa masu kokarin shiga fim har ma da wadanda ke ciki abokan aikinki?

Shawarar da zan bawa wanda suke tasowa da mu gabadaya har da ni me magana shi ne; ka san kanka, ka san darajar kanka, ka san na iyayenka, ka san na wanda ka ke rayuwa da su, kar ka yi abin da mutuncinka ya zube ko na ‘yan’uwanka ko na iyayenka ko ma dai kawayenka ace yau kana tare da wani a dalilinka ace ai wane ka-za ka-za yayi, a’a sai mun duba mun ga abin da ya dace duk abin da bai dace ba kar ma ka yi fostin din shi da za ka jawo wa kanka magana ko surutu ce-ce kuce, dole wani abu sai muna yi muna dubawa. Muna fatan kafin mu yi shi Allah ya kare mu duk wani abu da zai janyo mana zagin iyayen mu, ‘yan’uwan mu, Allah komai dadin shi ubangiji Allah kar ka ba mu ikon yin shi alfarmar Annabi Muhammad (s.a.w).

Me za ki ce ga jaridar Leadership Hausa har ma da wannan shafi na Rumbun Nishadi da sauran al’ummar da suke karanta wannan hirar taki?

Ina yi musu fatan alkhairi ubangiji Allah ya kara dauka su, Allah ya kara darajntasu a idon duniya gabadaya, Allah ya sa musu hannu a inda suke iyawa da inda ba sa iyawa, kuma ubangiji Allah ya yi musu abin da mai zato bai taba tsammani ba na alkhairi, tsakanina da su sai dai nayi fatan alkhairi, ina fatan alkairi a gare su sosai-sosai.

Ko kina da wadanda za ki gaisar?

Ba zai wuce masoya, ‘yan’uwa, da kowa da kowa ba, ina yi wa kowa da kowa fatan alkhairi ubangiji Allah ya bar mu tare, ya bar zumunci kuma roko na guda daya ga masoyana ‘yan’uwana duk wani abu ni dai Hauwa Ayawa kofa a bude take, socual media na za ka iya yi mun DM cikin ikon Allah zan yi maka ‘reply’ duk wani abu da ku ka ga nayi wanda bai dace bai kamata ba dan Allah dan Annabi ku bani shawara zan gyara cikin ikon Allah, dan Allah dan Annabi duk me nayi wanda ku ke ganin zai zubar da mutunci, ah wannan abu bai dace Hauwa’u tayi ba dan Allah dan Annabi ku bani shawara kuma zan yi zan bi, in sha Allahu, na gode Allah ya bar mu tare. Allah ya daukaka mu gabadaya kuma Allah ya kawo mana mazajenmu nagari.

Muna godiya, ki huta lafiya

Ni ma na gode sosai.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: Ayawa
ShareTweetSendShare
Previous Post

Hunan Ya Ruwaito Samuwar Karin 6.3% Na Kayayyakin Da Ake Fitarwa Zuwa Afirka Tsakanin Janairu Da Afrilu

Next Post

An Kaddamar Da Bikin Baje Kolin Aikin Gona Na Kasa Da Kasa Na Cote d’Ivoire

Related

Babban Burina A Harkar Fim Shi Ne Ganin Habakar Harshe Da Al’adun Hausa—Murtala Abdullah
Nishadi

Babban Burina A Harkar Fim Shi Ne Ganin Habakar Harshe Da Al’adun Hausa—Murtala Abdullah

1 day ago
Na Hadu Da Azzalumai Da Mayaudara Farkon Shigata Kannywood – Dan’duniya
Nishadi

Na Hadu Da Azzalumai Da Mayaudara Farkon Shigata Kannywood – Dan’duniya

1 week ago
Ko Maƙiyina Ba Na Yi Masa Fatan Tsintar Kansa A Halin Da Na Samu Kaina – Ummi Nuhu
Nishadi

Ko Maƙiyina Ba Na Yi Masa Fatan Tsintar Kansa A Halin Da Na Samu Kaina – Ummi Nuhu

2 weeks ago
Na Yi Lokacin Da Idan Aka Gan Ni Ake Gudu A Masana’antar Kannywood – Mai Dawayya
Nishadi

Na Yi Lokacin Da Idan Aka Gan Ni Ake Gudu A Masana’antar Kannywood – Mai Dawayya

2 weeks ago
An Ɗaura Auren Rahma Sadau A Kaduna
Nishadi

An Ɗaura Auren Rahma Sadau A Kaduna

2 weeks ago
Samun Kuɗi Ya Fi Samun Ɗaukaka Wahala A Kannywood -Baba Sadiƙ
Nishadi

Samun Kuɗi Ya Fi Samun Ɗaukaka Wahala A Kannywood -Baba Sadiƙ

3 weeks ago
Next Post
An Kaddamar Da Bikin Baje Kolin Aikin Gona Na Kasa Da Kasa Na Cote d’Ivoire

An Kaddamar Da Bikin Baje Kolin Aikin Gona Na Kasa Da Kasa Na Cote d’Ivoire

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Kama Mutane 69 Masu Fasa Bututun Mai A Yankin Neja-Delta

Sojoji Sun Kama Mutane 69 Masu Fasa Bututun Mai A Yankin Neja-Delta

August 25, 2025
Ƙungiyar KSCI Ta Nemi Sabon Tsari Don Magance Ƴan Bindiga A Katsina

Ƙungiyar KSCI Ta Nemi Sabon Tsari Don Magance Ƴan Bindiga A Katsina

August 25, 2025
Ƙungiyoyin Farar Hula Sun Nemi A Dakatar Da Jami’an Gwamnatin Kao

Ƙungiyoyin Farar Hula Sun Nemi A Dakatar Da Jami’an Gwamnatin Kao

August 25, 2025
Tinubu Ya Isa Brazil, Zai Nemi Masu Zuba Jarin Biliyoyi A Noma, Makamashi Da Fasaha

Tinubu Ya Isa Brazil, Zai Nemi Masu Zuba Jarin Biliyoyi A Noma, Makamashi Da Fasaha

August 25, 2025

Ɗaruruwan Mambobin APC Sun Sauya Sheka Zuwa ADC A Sokoto

August 24, 2025
Ƴansanda Sun Kama Wani Gawutaccen Ɗan Fashi Da Garkuwa Da Mutane A Nasarawa

Ƴansanda Sun Kama Wani Gawutaccen Ɗan Fashi Da Garkuwa Da Mutane A Nasarawa

August 24, 2025
Za A Bude Cibiyar Watsa Labarai Game Da Bukukuwan Nasarar Yaki Da Harin Japan 

Za A Bude Cibiyar Watsa Labarai Game Da Bukukuwan Nasarar Yaki Da Harin Japan 

August 24, 2025
An Kaddamar Da Makon Fina-finai Da Shirye-shiryen Talabijin Na SCO A Qingdao

An Kaddamar Da Makon Fina-finai Da Shirye-shiryen Talabijin Na SCO A Qingdao

August 24, 2025
CMG Za Ta Gabatar Da Bikin Faretin Soja Na Beijing Cikin Harsuna 85 Ga Duk Fadin Duniya 

CMG Za Ta Gabatar Da Bikin Faretin Soja Na Beijing Cikin Harsuna 85 Ga Duk Fadin Duniya 

August 24, 2025
Akwai Katin Zaɓe Fiye Da Dubu 367 Da Ba A Karɓa Ba A Kano – INEC

Akwai Katin Zaɓe Fiye Da Dubu 367 Da Ba A Karɓa Ba A Kano – INEC

August 24, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.