Gabanin zaben 2023, tsohon gwamnan Jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya bayyana yadda tsohon gwamnan jihar, Sanata Rabiu Kwankwaso, ya bata masa rai da magoya bayansa bayan komawarsa jam’iyyar NNPP a watan Mayu, 2022.
Shekarau, wanda ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Kano, a ranar Litinin, ya yi alkawarin bayyana matakinsa na karshe na sauya sheka nan da ‘yan kwanaki.
- Amurka Mai Satar Mai Daga Kasar Sham
- Ga Yadda Kasar Sin Ta Samu Ci Gaba Cikin Shekaru 10 Da Suka Gabata
Tsohon jigon jam’iyyar APC, wanda a halin yanzu yake wakiltar Kano ta tsakiya a majalisar dattawa, ya gana da babban kwamitin Shura, a karshen mako, inda suka tattauna kan batutuwan da suka shafi kudirin Atiku Abubakar na komawa PDP.
Kwamitin karkashin jagorancin Barista Habib Shehu, ya mika rahotonsa domin tantancewa.
Duk da cewa LEADERSHIP ba ta iya tabbatar da matakin da Shekarau zai dauka ba, amma akwai masu ra’ayin cewa zai iya komawa jam’iyyar PDP.