Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan zargin hannun Kwamishinan Sufuri na Jihar Kano, Alhaji Ibrahim Namadi, a batun karɓar beli ga mutumin da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi, Sulaiman Aminu Danwawu.
Wannan umarni ya biyo bayan karɓar ƙorafe-ƙorafen jama’a bayan ɓullar rahotanni sun bayyanar da sunan kwamishinan a takardun kaɓar belin wanda ake zargi.
- Namadi Sambo Ya Yaba Wa Gwamna Abba Yusuf Kan Bunƙasa Ɓangaren Ilimi Da Gine-Gine A Kano
- Abba Ya Yi Sabbin Naɗe-naɗe A Jihar Kano
Mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar.
Don ɗaukar mataki kan batun, Gwamna Yusuf ya kafa kwamitin bincike na musamman a ƙarƙashin jagorancin Barrista Aminu Hussain, mai ba shi shawara kan harkokin Shari’a da Tsarin Mulki.
An umarci kwamitin da ya binciki dukkan abubuwan da suka shafi lamarin tare da bayar da shawarwarin da suka dace cikin gaggawa.
Mambobin kwamitin sun haɗa da:
1. Barr. Aminu Hussain – Shugaba
2. Barr. Hamza Haladu – Mamba
3. Barr. Hamza Nuhu Dantani – Mamba
4. Alhaji Abdullahi Mahmoud Umar – Mamba
5. Manjo Janar Sani Muhammad (Rtd.) – Mamba
6. 6. Kwamared Kabiru Said Dakata – Mamba
7. Hajiya Bilkisu Maimota – Sakatariya
Yayin da yake sanar da kafa kwamitin, Gwamna Yusuf ya nuna matuƙar damuwarsa game da zargin da ke kan jami’in gwamnati, tare da jaddada aniyarsa ta yaƙi da safarar miyagun ƙwayoyi da duk wasu munanan ɗabi’un da ba su dace ba a fadin jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp