Tawagar ƙwallon ƙafa ta mata a Nijeriya (Super Falcons) za ta buga wasan ƙarshe na gasar kofin ƙasashen Afirika yau da ƙasar Moroko a filin wasa na Olympique da ke birnin Rabat na ƙasar Moroko, za a buga wasan da misalin ƙarfe 9 na dare agogon Nijeriya.
Wannan ne karo na biyu da ƙasashen biyu za su haɗu a tarihi, sun haɗu a karon farko a shekarar 2022 a wasan kusa da na ƙarshe na gasar kofin ƙasashen Afirika na mata, inda Moroko ta fitar da Nijeriya bayan bugun Fenarati, a wannan karon duka ƙasashen biyu na daga cikin waɗanda ake hasashen za su iya lashe kofin, duba da cewa babu kanwar lasa a cikinsu.
- Kano Pillars: Yaushe Kungiyoyin Kwallon Nijeriya Za Su Daina Shiga Matsalar Kudi?
- Kwallon Mata: Nijeriya Ta Nuna Wa Afrika Ta Kudu Kwanji A Pretoria
Idan Nijeriya ta samu nasarar lashe kofin zai kasance karo na 10 kenan da ta lashe kofin a tarihi, idan kuma Moroko ce ta yi nasara zai kasance na farko da ƙasar ta Arewacin Afirika ta taɓa lashewa, hukumar ƙwallon ƙafa ta Afirika (CAF) za ta bai wa duk wanda ya lashe gasar zunzurutun kuɗi har Dala miliyan 1, yayin da wanda ya zo na biyu zai samu Dala 500,000.
Tsohon kocin Sifaniya Jorge Vilda ke jagorantar tawagar Moroko, yayin da Justin Madugu ke jagorantar Nijeriya, wadda ke kan gaba wajen iya taka leda a nahiyar, ta samu nasarar doke Afrika ta Kudu mai riƙe da kofin gasar a yayin da Moroko ta fitar da ƙasar Ghana.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp