Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya halarci taron kasa da kasa na manyan jami’ai, game da jagorancin fasahar kirkirarriyar basira ko AI a matakin kasa da kasa, wanda ya gudana yau Asabar a birnin Shanghai, inda ya kuma gabatar da jawabi.
A cikin jawabinsa, Li Qiang ya ba da shawarwari guda uku, kan yadda za a yi amfani da kayayyakin fasahar AI, da sa kaimi ga raya fasahar AI, da kuma sarrafa harkokin fasahar AI.
- Yadda Masu Bukata Ta Musamman Suka Rungumi Sabbin Dabarun Noma Domin Ciyar Da Kansu
- ‘Yancin Gashin Kai: Ma’aikatan Kananan Hukumomi Sun Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki
Na farko, ya ce kamata ya yi a kara mai da hankali ga amfani da fasahar AI tsakanin dukkan al’ummun kasa da kasa, da samar da moriya tare daga fasahar. Na biyu kuma a kara yin hadin gwiwa wajen kirkire-kirkire, don samun karin nasarori a fannin fasahar AI. Sai na uku, wato a sarrafa harkokin fasahar AI tare, don tabbatar da fasahar ta amfani dukkanin bil’adama.
Ya ce, kasar Sin na dora muhimmancin gaske ga batun sarrafa harkokin fasahar AI a dukkanin duniya, da shiga hadin gwiwa tsakanin bangarori daban daban, kana tana son kara samar da gudummawa, da rarraba fasahohin da ta samu ga sassan kasa da kasa. Hakazalika, gwamnatin kasar Sin ta yi kira da a kafa kungiyar hadin gwiwar fasahar AI ta duniya.
An bude taron ne a birnin Shanghai na gabashin kasar Sin bisa jigon “Hadin kan duniya a zamanin basirar AI”, ana kuma sa ran a bana, taron zai mayar da hankali ga yayata tasirin sassan kasa da kasa, da hallara tarin masu ruwa da tsaki, da fadadar filin baje kayayyaki, da gabatar da sabbin kayayyaki.
A karon farko, filin baje hajoji masu nasaba da taron ya kai sama da sakwaya mita 70,000, kana adadin kamfanoni mahalarta taron sun haura 800, yayin da aka gabatar da kayayyaki sama da 3,000, wadanda suka hada da manyan na’urori da masu amfani da fasahar AI, da mutum-mutumin inji. Kana an gabatar da sabbin kayayyaki sama da 100 da aka gabatar da su a karon farko.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp