Fasahar kirkirarriyar basira ta AI na ci gaba da bullo da fasahohi daban-daban a rayuwarmu ta yau. Daya daga cikin abubuwan burgewa game da hakan a kasar Sin shi ne fasahar da aka nuna wajen shirya wasan kwallon kafa da aka fafata a tsakanin mutum-mutumi masu siffar dan’adam a makwannin da suka gabata.
An saba ganin wasan kwallon kafa na wasannin bidiyo (video games) wadda mutane suke sarrafawa daga na’urar da ake buga wasan a ciki. Amma wasan mutum-mutumin da nake magana a kai ya bambanta da wannan, domin maimakon sarrafawa daga waje, a wannan, ’yan kwallo na mutum-mutumin ne suke sarrafa kansu. An saka musu kwakwalwa mai auna yanayi mai sarkakiya da kawo mafita a kan lokaci, da hankalto tunani mai kyau da iya mu’amala da juna cikin hadin gwiwa, da amfani da dabarun neman galaba a kan abokan karawa tamkar dai yadda ’yan kwallon mutane suke yi a cikin fili.
- Rashin Nasarar DPP A Zagayen Farko Na Kuri’ar Kiranye Ya Nuna Rashin Amincewar Al’ummar Taiwan Da Salon Mulkin Jami’yyar
- Mataimakin Firaministan Kasar Sin Ya Yi Kira Da A Karfafa Hadin Gwiwar Sin Da Amurka
Bugu da kari, an kera ’yan wasan da jiki mara nauyi ta yadda za su kasance cikin karsashi a fagen wasa da kuma nuna juriya. Fasahar kirkirarriyar basira ta AI da aka sa a jikin ’yan wasan na mutum-mutumi ita ce ta ba su damar kula da dokokin wasan, da amfani da fikirar jefa kwallo da matakan tsare gida wadda gaba daya ‘yan wasan ne suka tsara wa kansu ba wani daga gefe ba.
Ba kamar mutum-mutumin da suka yi tseren gudu ko wasan damben boksin wadanda aka rika tafiyar da su daga gefe ba, wadannan ’yan wasan kwallon; kowa a cikinsu shi ya rika sarrafa kansa ba tare da taimakon wani dan’adam ba. Hatta faduwa idan sun yi a filin wasa da kansu suke mikewa tare da ci gaba da buga wasa.
An samu wannan babbar nasara ce ta barin ’yan wasan su sarrafa kansu bisa amfani da matakan gudanarwa na na’ura mai kwakwalwa guda uku, kamar yadda babban jami’in samar da ‘yan wasan mutum-mutumin da suka fafata a gasar Cheng Hao ya bayyana. Mataki na farko shi ne na tunani da hasashe, na biyu shi ne na sarrafa motsi, sannan na uku ya kunshi yanke hukunci kan abin da ya dace a aikata.
Wadannan ’yan wasan kwallon kafa na mutum-mutumi sun sake nuna bajintar da kasar Sin ke nunawa a fagen kere-keren mutum-mutumi masu siffar dan’adam da kuma yadda masana’antar bangarensu ke samun ci gaba cikin hanzari a kasar.
A watan Agusta mai kamawa ne kasar Sin za ta karbi bakuncin gasar wasannin motsa jiki na mutum-mutumi masu siffar dan’adam. Kuma wannan wasan kwallon kafa na mutum-mutumi da aka gwabza fafatawar karshe a dandalin wasannin motsa jiki na fasahar zamani da ke birnin Beijing, wata kyakkyawar shaida ce a kan yadda kasar ta shirya wa karbar bakuncin wannan gasa. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp