ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Mutanen Katsina Sun Koka Kan Dakatar da Aikin Gyaran Hanyar Mararrabar Kankara–Dutsinma–Katsina

by Abubakar Sulaiman
11 months ago
Katsina

Mazauna yankin da ke kan hanyar Mararrabar Kankara–Dutsinma–Katsina sun nuna rashin jin daɗi kan dakatar da aikin gyaran babbar hanyar, inda suka zargi Ibrahim Kabir Masari, mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin siyasa, da kuma Gwamna Dikko Umar Radda da hannu wajen soke kwangilar saboda dalilan siyasa.

Mutanen ƙauyuka irin su Birchi, da Burdugau, da Yargoje, da Tudu da Yantumaki sun bayyana cewa wannan mataki ya bar hanya cikin mummunan yanayi, duk da cewa ɗaya daga cikin hanyoyin da aka fi amfani da su a jihar Katsina. Aikin wanda ya kai kimanin ₦147.6 biliyan, an bai wa kamfanin Vipan Global Investment Resources Ltd kwangilar a watan Afrilu 2024 tare da amincewar Majalisar Zartarwa ta Ƙasa (FEC), kafin Ma’aikatar Aiyuka ta bayar da umarnin dakatar da aikin a watan Yuli bisa hujjar “rashin kuɗi.”

  • Gwamnatin Katsina Ta Ƙara Samar Da Dakarun Tsaro 200 Domin Maganace Ta’addanci
  • Tinubu Ya Amince Da Tallafin Naira 250,000 Ga Ƙananan ’Yan Kasuwa A Jihar Katsina

Sai dai mazauna yankin sun yi watsi da wannan hujja, suna zargin Ministan Aiyuka, David Umahi, da bin umarnin Masari da Radda saboda suna ganin kamfanin yana da alaƙa da jam’iyyar adawa ta PDP. Wani matashi daga Yantumaki, Tanko Bello, ya ce, “Dole ne kowa ya zama ɗan jam’iyya mai mulki kafin a yi masa aiki? Dukkanmu ‘yan ƙasa ne masu cancantar samun kulawar gwamnati.”

ADVERTISEMENT

Mazauna yankin sun kuma ce dakatar da aikin ya ƙara tsananta matsalar tsaro, ya takaita kasuwanci, tare da haifar da haɗura akai-akai. Sun yi gargadin cewa wannan lamarin zai iya rage farin jinin jam’iyyar APC a jihar Katsina kafin zaɓen 2027. “Wannan abu raini hankalin jama’a ne,” in ji wani ɗan ƙasa. “Zamu nuna rashin jin daɗinmu lokacin da ya dace.”

Sun roƙi Shugaba Bola Tinubu da ya sa baki don dawo da aikin, suna bayyana matakin a matsayin abin kunya da zai iya lalata martabar gwamnatinsa a idanun jama’a.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

Katsina
Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Iyalin El-Rufai Sun Bai Ministan Tsaro Wa’adin Kwana 7 Kan Zargin Rikicin Kudancin Kaduna
  • Abubakar Sulaiman
    Atiku Ya Zargi Gwamnatin Tarayya Da Cin Bashi Kamar Mashayin Da Kuɗi Ya Ƙarewa
  • Abubakar Sulaiman
    Boko Haram Ta Kai Hari Adamawa, Ana Fargabar Mutuwar Mutane 11
  • Abubakar Sulaiman
    Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Sokoto, Sun Kashe Mutane 7, Sun Yi Garkuwa Da 12

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
Shugaba Tinubu Ya Gana Da Sabbin Hafsoshin Tsaro

Shugaba Tinubu Ya Gana Da Sabbin Hafsoshin Tsaro

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.