An yi sabon zagayen tattaunawar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka a birnin Stockholm na Sweden a ranakun 28 da 29 ga watan nan. Inda bangarorin biyu suka amince da tsawaita adadin kwanaki 90 da aka tsayar, na dakatar da karin harajin ramuwa da Amurka ta dora kan hajojin Sin dake shiga kasar kan kaso 24 bisa dari, da kuma dakatar da matsayar Sin ta daukar matakan martani kan harajin.
An yi hasashen cewa, wannan matsayar bai daya da bangarorin Sin da Amurka suka cimma ta samar da karin damammaki ga kiyaye tattaunawarsu, yayin da suke cikin mawuyacin halin warware sabanin tattalin arziki da cinikayya a tsakaninsu kwata-kwata. Lamarin da ya yi daidai da burin kasashen duniya, yayin da hakan zai ba da tabbaci ga tattalin arzikin duniya.
Ta yaya Sin da Amurka za su inganta hadin kansu don samun karin nasarori tare? Ya kamata tsarin tattaunawar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka ya taka muhimmiyar rawa, ganin yadda hakan ya ba da tabbaci ta fuskar tsare-tsare ga sassan biyu, wajen kawar da bambancin ra’ayi da inganta hadin kansu.
Matakan da za a dauka na da muhimmanci sosai wajen aiwatar da matsayar bai daya da aka cimma. Abu na farko da ya kamata Amurka ta yi shi ne kawar da duk wata gurguwar fahimta kan kasar Sin. Bisa wannan tushe, ya kamata Amurka ta aiwatar da matsayar bai daya da sassan biyu suka cimma cikin tsanaki da kuma rike amana. Ban da wannan kuma, kamata ta yi gwamnatin Amurka ta kara sauraron ra’ayoyin masana’antu. Alal hakika, ainihin dangantakar cinikayya tsakanin Sin da Amurka, shi ne cimma moriyar juna da samun nasara tare. Yayin da hadin kansu kuma shi ne zabi daya tilo mafi dacewa. (Kande Gao)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp