Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya shelanta cewa; yarjejeniyar dala biliyan daya da Nijeriya ta ƙulla da ƙasar Brazil, ƙarƙashin shirin noma na GIP, za ta buɗe wani sabon babi na taimaka wa wajen ƙara bunƙasa aikin noma a Nijeriya, musamman ta hanyar amfani da kayan noma na zamai.
Kazalika, ya ce; za ta kuma taimaka wajen ƙara samar da ayyukan yi da kuma ƙara samar da wadataccen abinci a ƙasar.
Tinubu ya bayyana haka ne, lokacin da ya karɓi baƙuncin Mataimakin Shugaban ƙasar Brazil, Geraldo Alckmin, a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
- Yaki Da Talauci: Yadda Kasar Sin Ke Taka Rawar Gani A Duniya
- Yaki Da Talauci: Yadda Kasar Sin Ke Taka Rawar Gani A Duniya
“Shrin, wanda Ma’aikatar Aikin Noma da Samar da Wadataccen Abinci ta wannan ƙasa ta yi hadaka da Ma’aikatar Kula da Harkokin ƙasashen Waje ta Brazil da kuma masu ruwa da tsaki masu zaman kansu, an tsara hakan ne kan yadda za a farfaɗo da tsarin aikin noma a wannan ƙasa”, in ji Tinubu.
A cewarsa, za a gudanar da shirin ne, ta hanyar yin amfani da kayan noma na zamani tare da samar da cibiyar bayar da horo, wanda hakan zai taimaka wa Nijeriya, ta iya ciyar da ƴan ƙasar da abinci da kuma kai wanda ya yi rara zuwa kasuwannin da ke ƙasashen Afirka, don sayawa.
Shugaban ya kuma bayar da tabbacin yin hadaka da Brazil ɗin a wasu manyan ɓangarori, ciki har da ɓangaren noma, domin samun riba da sauransu.
Tinubu ya kuma jinjina wa kamfanonin ƙasar ta Brazil, musamman kamar irin su; A.P. Moller–Maersk da kuma Grundfos, kan gudunamawar da suke ci gaba da bai wa Nijeriya a ɓangaren samar da kayan aiki da tsarin aikin noma da kuma gudunmawar da suka bayar, domin a tallafawa masu gudun hijara na wannan ƙasa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp