A cikin fiye da shekaru 60 da suka gabata, jihar Xizang mai cin gashin kanta dake kudu maso yammacin kasar Sin ya samu ci gaban da ya kafa tarihi a fannin tattalin arziki da zamantakewa tun bayan kafa ta a shekarar 1965. Wani jami’an jihar ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya gudanar a yau Talata.
Jami’ai sun bayyana sauyin da jihar ta samu daga wata jiha mai fama da talauci zuwa jihar al’umma mai ci gaban zamani, wadda ke tattare da bunkasar tattalin arziki da ba a saba ganin irinsa ba, da inganta jin dadin rayuwar al’umma, da kuma kiyaye al’adunta na musamman.
A cewar sakataren kwamitin jihar Xizang mai cin gashin kanta na jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin Wang Junzheng, ya zuwa shekarar 2024, karfin tattalin arzikin Xizang na GDP ya haura Yuan biliyan 276.5 kwatankwacin dalar Amurka biliyan 38.5, wanda ya ninka na shekarar 1965 sau 155, inda hakan ya nuna karuwarsa da kashi 8.9 a mizanin duk shekara.
Kazalika, kudaden kasafin kudi na jihar sun karu da ninki 1,258, inda suka tasamma yuan biliyan 27.7. Bugu da kari, baya ga bunkasa tattalin arziki, an samu gagarumin ci gaba wajen inganta rayuwar al’umma.
Wang ya kara da cewa, jihar Xizang ta fatattaki talauci gaba daya, kuma a halin yanzu tsarinta na ilimi yana ba da ilimi kyauta na tsawon shekaru 15 daga matakin kindergarten zuwa sakandare. Sannan an fadada yadda ake kula da kiwon lafiyar jama’a, tare da tsammanin adadin shekarun da mutum zai rayu na iya kaiwa 72.5. Bayan haka, an kara habaka ci gaban birane, tare da kafa garuruwa na zamani a sassan yankin tudu, yayin da kuma aka kiyaye al’adun gargajiya na Tibet yadda ya kamata. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp