Babban bankin kasar Sin ya bayyana cewa, kasar ta fitar da wasu ka’idoji don karfafa nuna goyon baya ga sabbin masana’antu ta hanyar hada-hadar kudi.
Ka’idojin da babban bankin na jama’ar kasar Sin da wasu sassan gwamnati shida suka fitar a jiya Talata, sun bayyana cewa, ya kamata a samar da tsarin hada-hadar kudi domin masana’antu masu ci gaba irin na zamani da ke aiki da makamashi mai tsafta nan da shekarar 2027.
A bisa bayanan ka’idojin, an nuna cewa, ya kamata a cika dukkan muradun bashin da masana’antun ke bukata ya zuwa shekarar 2027, tare da samun adadi mai yawa da mabambantan manyan basussukan da za a bayar ba tare da yankewa ba, kana a samu babban ci gaba ta fuskar kara yawan jarin kamfanoni daga kudaden masu zuba jari.
Har ila yau, an bayyana cewa, ya kamata a dauki matakai na inganta amfani da kudi wajen cimma muhimman nasarorin fasaha, da samar da kudi na dogon lokaci, da habaka jarin da ake zubawa na dogon wa’adi don hanzarta sayar da sabbin fasahohin kimiyya da ake samu, da karfafa harkokin kudi na manyan kamfanoni domin bunkasa samar da tsare-tsare masu aminci na dogaro da kai ga masana’antu.
Ka’idojin sun kuma nemi a yi kokarin amfani da hada-hadar kudi wajen tallafa wa daga darajar tsofaffin masana’antu, da fadada masana’antu masu tasowa, da kuma tsara dabarun kafa masana’antu na gaba. (Mai Fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp