Ofishin jakadancin kasar Sin a Birtaniya, ya yi tir da kausasan kalamai kan rahotannin dake cewa tsohon firaministan Birtaniya Boris Johnson ya ziyarci yankin Taiwan na Sin da kiran da ya yi wa kasashen yamma su kulla huldar tattalin arziki da yankin.
Wani kakakin ofishin jakadancin ya bayyana a jiya cewa, suna adawa matuka da duk wata ziyara da wani dan siyasar Birtaniya zai kai Taiwan bisa ko wane dalili.
Kakakin ya kuma nanata cewa, Taiwan bangaren kasar Sin ne da ba zai iya ballewa ba, kana batutuwan da suka shafi yankin, batutuwa ne na cikin gidan Sin da ba sa bukatar katsalandan daga waje.
Bugu da kari, ofishin jakadancin ya ce babbar barazana ga tsaro da zaman lafiyar Zirin Taiwan shi ne ingiza neman ballewa na mahukuntan yankin, yana mai cewa, Sin ba za ta taba bari wani ya raba Taiwan da kasar ba ta kowace hanya. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp