Hausawa su kan ce “Karen bana shi ke maganin zomon bana”, don nuna cewa matasa ne suke iya daidaita matsalolin da ake fuskanta a zamanin da muke ciki. A duk lokacin da na tuna da maganar da wani abokina dan Najeriya, ya kan ce, “Matasa su ma sun haifar da dimbin matsaloli”. To, a ganina, wadannan matasa dama kawai suke bukata ta raya kansu, da nuna kwarewarsu.
A kwanan baya, kasar Sin ta gudanar da wata gasar daliban jami’o’i ta fuskar kirkiro sabbin fasahohi, a kasar Kenya, wadda ta zama wata kyakkyawar dama ga matasan kasashen Afirka. A wajen gasar da jami’ar koyon ilimin noma ta birnin Nanjing na kasar Sin ta karbi bakuncinta, wasu tawagogi 30 daga jami’o’i 21 na kasashe 9 dake nahiyar Afirka sun samu lambobin yabo.
- Nijeriya Da Indiya Za Su Haɗa Kai Wajen Yaƙi Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi
- Al Hilal Za Ta Biya Yuro Miliyan 53 Don Ɗaukar Nunez Daga Liverpool
Cikin abubuwan da aka kirkiro wadanda suka samu lambar yabo, akwai wani sabon nau’in leda da ake amfani da ita wajen rufe gonaki don adana ruwa a cikin kasa, da wasu dalibai ‘yan kasar Kenya suka kirkira; da wata sabuwar fasahar samar da sabon nau’in tumatir da ya dace da muhallin kasashen Afirka, da wasu daliban kasar Tanzania suka tsara. Ban da haka kuma, akwai inji mai sarrafa kansa wanda ke iya bambanta kunshin sakonni da kuma raba su, da wasu dalibai na kasar Habasha suka tsara; gami da wani sabon nau’in abincin kaza mai matukar araha, da wasu daliban kasar Ghana suka kirkira, da dai sauransu. Ta hanyar dandalin da kasar Sin ta samar, wadannan matasan kasashen Afirka sun nuna hazakarsu, tare da samar da gudunmowa ga yunkurin raya kimiyya da fasaha a nahiyar Afirka.
Sa’an nan, hakika idan mun yi tunani kan abun da ya sa aka shirya gasar, to, za mu fahimci cewa, hadin gwiwar Sin da Afirka wata kyakkyawar dama ce ga matasan kasashen Afirka, a fannin raya kansu.
Mun san cewa, ci gaban harkokin matasa na bukatar bunkasar sana’o’i. Cikin shekarun nan, aikin zuba jari ga kasashen Afirka da kasar Sin ke yi na samun ci gaba yadda ake bukata. Inda yawan kudin da Sin take zubawa kai tsaye a fannin samar da kayayyaki a kasashen Afirka, ya kai fiye da dalar Amurka miliyan 400 a duk shekara. Kana darajar hadin kan bangarorin Afirka da Sin ta fuskar gina kayayyakin more rayuwa, ta kai fiye da dala biliyan 37 a duk shekara. Hadin gwiwar bangarorin 2 ya shafi zirga-zirgar ababen hawa, da aikin gona, da makamashi, da tattalin arziki mai alaka da fasahohin zamani, da fasahohin bunkasa tattalin arziki ba tare da gurbata muhalli ba, da dai sauransu, ta yadda ya taimaki kokarin raya masana’antu da habaka tsarin tattalin arziki zuwa fannoni daban daban a kasashen Afirka, da samar da dimbin guraben aikin yi, gami da damammakin raya sana’o’i ga matasan kasashen.
Ban da haka, ci gaban harkokin matasa ba zai rasa alaka da karuwar ilimi da ingantuwar fasahohi ba, inda a wannan fanni ma kasar Sin ta tsara ayyukan hadin kai da yawa, don samar da damammakin samun horon fasahohin sana’o’i ga dimbin matasan Afirka, da horar da kwararrun masana matasa masu ilimin aikin gona da masu jagorantar aikin wadatar da manoma ta wasu sabbin fasahohi a kasashen Afirka, da kafa cibiyoyin bude sabbin kamfanoni da kirkiro sabbin fasahohi na matasa, da kulla huldar hadin kai tsakanin jami’o’i dari 1 na kasashen Afirka da kasar Sin, da dai sauransu. Inda gasar da muka ambata ita ma take cikin ayyukan da aka tsara tare da aiwatar da su.
Sande Ngalande, darakta ne na cibiyar nazarin batutuwa masu alaka da shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” ta jami’ar Zambia. Ya taba bayyana cewa, dabarar kasar Sin ta zamanantar da kasa ta amfani kasashen Afirka, inda dimbin matasan Afirka masu sana’o’i daban daban ke son mu’ammala da Sin, da fahimtar Sin, da koyon fasahohin kasar Sin. Kana ta hanyar hadin gwiwar Sin da Afirka, matasan Afirka suna iya kulla zumunci mai zurfi da Sinawa, gami da samun damar raya kansu, da kasashensu, da tabbatar da ci gaba mai dorewa a nahiyar Afirka.
Cikin shirin ajandar shekarar 2063 na kungiyar kasashen Afirka ta AU, an ce ya kamata a sanya matasa su zama karfin farfado da nahiyar Afirka, kuma hadin gwiwar Sin da Afirka na taimakawa wajen ganin tabbatuwar wannan buri a zahiri. (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp