Kasar Sin ta sanar a yau Alhamis cewa ta yi nasarar kammala cikakken gwajin sauka da tashin kumbun binciken a duniyar wata mai dauke da bil adama, a wani yankin gwaji dake gundumar Huailai ta lardin Hebei.
Gwajin da aka kammala ranar Laraba na nuni da wani muhimmin ci gaban da Sin ta samu a bangaren shirinta na binciken duniyar wata, kuma shi ne karon farko da Sin ta gudanar da gwajin sauka da tashin kumbu mai dauke da dan adama, a wajen duniyar dan adam. (Fa’iza Mustapha)














