Wasu yara maza uku sun rasa rayukansu bayan sun faɗa cikin wani tafki da ke bayan Asibitin Gabaɗaya na Monguno da ke Jihar Borno, a ranar Alhamis.
A cewar wata majiya, waɗanda suka mutu sun haɗa da Mallam Gana Mohammed, da Modu Audu Saleh da kuma Abba Ngumami, dukkansu mazauna sansanin ‘yan gudun hijira na Water Board da ke Monguno.
- Majalisar Dattawa Ta Yi Allah-wadai Da Zanga-zangar Ƙin Jinin ’Yan Nijeriya A Ghana
- ‘Yansanda Sun Kuɓutar Da ‘Yan Ghana 19 Da Aka Yaudare Su Zuwa Nijeriya
Mahaifin ɗaya daga cikin yaran, Muhammed Aisami, ya bayyana cewa yaran sun tafi yin wanka ne da misalin ƙarfe 7:40 na safe lokacin da lamarin ya faru.
Tuni ma’aikatan ceto da jami’an ‘yansanda suka isa wurin inda tare da masu jaje aka ciro gawarwakin yaran batan kuma kai su Babban Asibitin Monguno, likitoci suka tabbatar da mutuwarsu, tare da shaida cewa babu wata alamar rauni a jikinsu.
Kawo yanzu dai an miƙa gawarwakin ga iyayesu don gudanar da jana’izasu bisa tsarin Musulunci.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp