Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya ce ma’aikatar harkokin wajen kasar, da ofishin jakadancin kasar a Philippines, sun gabatar da korafi da babbar murya dangane da kalaman da aka jiyo jagoran Philippines na yi game da batun yankin Taiwan na Sin.
Kakakin wanda ya bayyana hakan a Juma’ar nan, ya ce, yayin ziyarar da ya gudanar a kasar India, shugaban na Philippine ya shaidawa ‘yan jarida cewa, idan har yaki ya barke tsakanin Sin da Amurka, tabbas kasarsa za ta shiga, saboda kasancewarta a kewayen yankin, da ma ‘yan Philippines da dama dake zaune a Taiwan, wadanda ya zama wajibi a aiwatar da matakan mayar da su gida.
Jami’in Sin ya kara da cewa kasar Sin daya ce tak a duniya, kuma Taiwan bangare ne na Sin da ba za a iya balle shi ba. Kazalila, batun Taiwan harka ce ta cikin gidan kasar Sin, kuma tushe na babbar moriyar kasar. Don haka warware batun yankin na Taiwan na wuyan kasar Sin ita kadai, kuma ba za ta taba hakuri da tsoma hannun wasu sassan waje ba. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp