Wani rikici ya ɓarke a ƙaramar hukumar Bogoro, Jihar Bauchi, inda wani manomi mai suna Irmiya Yohanna, mai shekara 40 daga ƙauyen Kaduna-Bogoro, ya rasa ransa.
Lamarin ya faru ne a ranar Juma’a lokacin da ya tafi gonarsa, bai dawo gida ba, daga baya aka same shi a mace a cikin gonar.
- An Bude Taron Mutum-Mutumin Inji Na Duniya Na 2025 A Yau Juma’a
- ‘Yansanda Sun Kama Mutane 302, Sun Ceto Mutum 50 Da Aka Sace A Katsina
Bayan mutuwarsa, wasu fusatattun matasa suka kai hari kan dabbobin Fulani a yankin, inda suka kashe shanu 20 da tumakai 19, sannan suka jikkata wasu dabbobi da dama.
Rundunar ‘yansandan Bauchi ta ce bayan samun rahoton, jami’ansu ƙarƙashin SP Fitoka Golda sun isa wajen, suka ɗauki gawar marigayin zuwa babban asibitin Bogoro, inda likita ya tabbatar da mutuwarsa.
Binciken farko ya nuna cewa rikicin ya fara ne bayan da Irmiya ya tarar da shanu a gonarsa, ya buƙaci makiyayan su fita, sai faɗa ya kaure har ta kai ga mutuwarsa.
‘Yansanda sun kama wani da ake zargi da hannu a kisan, mai suna Ahmadu Mairiga, kuma sun ceto shanu 249.
Kwamishinan ‘yansandan Bauchi, CP Sani-Omolori Aliyu, ya ziyarci yankin, ya gana da shugabannin Fulani, sarakuna da shugabannin al’umma, inda ya gargaɗi mazauna yankin da su guji kawo tashin hankali, tare da tabbatar da cewa an ɗauki matakan tsaro don hana sake faruwar irin haka.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp