An ɗaura auren shahararriyar jarumar Kannywood, Rahma Sadau, da mijinta Ibrahim Garba, a Jihar Kaduna yau Asabar.
An yi bikin da safe a masallacin Atiku Auwal da ke Ungwan Rimi, inda ‘yan uwa da abokan arziƙi suka halarta.
- Kasar Duniyar Wata Da Kasar Sin Ta Samo Ta Samar Da Sakamakon Nazari Fiye Da 150
- An Naɗa Farfesa Adamu Muƙamin Mataimakin Shugaban Jami’ar Yakubu Gowon, Abuja
Rahma ta zaɓi yin bikin cikin natsuwa domin kauce wa hayaniya.
Bayan labarin ya bayyana a kafafen sada zumunta, ta tabbatar da ɗaura auren nata.
Rahma ta shahara a fina-finan Kannywood da kuma wasu daga cikin fina-finan Nollywood.
Bayan da aka ɗaura auren, masoyanta da abokan aikinta suka tura mata saƙonni taya murna daga sassa daban-daban na Nijeriya.
Wannan aure ya zo watanni kaɗan bayan rasuwar mahaifinta, wanda ya rasu bayan gajeriyar rashin lafiya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp