Yanzu haka mutane huɗu suna karɓar magani a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Shika, Zariya, bayan sun jikkata a wani mummunan haɗarin da ya haɗa da tankoki biyu a ƙauyen Kake, yankin Dan Magaji, kan hanyar Zariya–Kaduna. Haɗarin ya jawo mummunar gobara bayan haɗuwar motocin.
Kwamandan hukumar kiyaye haɗɗura ta ƙasa (FRSC) reshen Zariya, Nasir Abdullahi Falgore, ya bayyana cewa ɗaya daga cikin tankokin na ɗauke da iskar gas (LNG), yayin da ɗayar kuma babu komai a cikinsa. Ya ce sakamakon binciken farko ya nuna tayar ɗaya daga cikin tankokin ce ta fashe, lamarin da ya sa tankar da ke biye ta bugi ta gaba, wanda ya haddasa fashewar gas da tayar da gobara.
- Kwalejin Digiri Na Biyu Ta ABU Ta Ƙaddamar Da Sabbin Ɗalibai A Zariya
- Shirin Iskar Gas Na CNG Abin A Yaba Wa Shugaba Tinubu Ne -Shugaban IPMAN Na Ƙasa
Kwamandan hukumar kashe gobara ta ƙasa a Zariya, Aminu Ahmadu Kiyawa, ya ce jami’ansa sun isa wurin cikin gaggawa bayan samun kiran wayar gaggawa. Ya tabbatar da cewa mutum uku sun jikkata sakamakon fashewar gas, yayin da aka ceto mutum guda daga ɗaya tankar, kuma duka huɗun an garzaya da su zuwa asibitin ABU domin samun kulawar likitoci.
Kiyawa ya ƙaryata jita-jitar da ake cewa haɗarin ya rutsa da ƙananan motoci irin su Gulf, yana mai cewa “Lokacin da muka isa wurin, tankoki biyu ne kawai muka gani. Babu wata ƙaramar mota da ta shiga hatsarin.” Shaidun gani da ido ma sun tabbatar da cewa tankoki biyu kacal ne suka shiga haɗarin, kuma babu wanda ya rasu a lokacin da ake haɗa wannan rahoton.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp