Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasa (EFCC) ta yi wa tsohon gwamnan Jihar Sokoto, Sanata Aminu Tambuwal, tambayoyi kan zargin fitar da wasu kuɗi har Naira biliyan ₦189 ta hanyar cire kuɗin daga banki.
Rahotanni sun nuna cewa, Tambuwal ya isa shalƙwatar EFCC a Abuja da misalin karfe 11:30 na safiyar yau Litinin, inda yake ci gaba da fuskantar tambayoyi daga jami’an bincike kan zargin. Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a tabbatar ko za a tsare shi ba na dogon lokaci ba.
- Ku Yaƙi Cin Hanci Ba Ƴan Adawa Ba – ADC GA EFCC
- EFCC Ta Kama Mutane 11 Kan Haƙar Ma’adinai Ba Bisa Ƙa’ida Ba A Akwa Ibom
Majiyoyi daga EFCC sun tabbatar da cewa an tsare shi ne kan zargin fitar da kuɗi a bainar jama’a wanda ke saɓawa dokar hana safarar kudi masu nauyi ta shekarar 2022. An ce, “Mun ware dukkan zarge-zargen da suka shafi Tambuwal, saura ya bayar da bayani.”
Kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya ƙi yin bayani kan lamarin lokacin da aka tuntuɓe shi. Ana sa ran tsohon gwamnan zai bayar da amsa kan yadda aka samu irin waɗannan manyan fitar kuɗi a lokacin mulkinsa a Jihar Sokoto.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp