Shahararren dan wasan kwallon kafa na kasar Portugal, Christiano Ronaldo, ya nemi auren budurwar da suka dade a tare Georgina Rodríguez.
Rodríguez ce ta wallafa labarin neman aurenta da Ronaldo ya yi a shafinta na Isntagram inda aka ga tsohon dan wasan na Manchester United ya saka mata zobe a hannu.
- Sin Ta Gabatar Da Sanarwar Hadin Gwiwa Kan Taron Tattalin Arziki Da Cinikayya Tsakaninta Da Amurka A Stockholm
- PDP Ta Soki Gwamnatin Tinubu Kan Tsare Tambuwal Da EFCC Ta Yi
“En na amince a yanzu da kuma karshe ln rayu da shi” Georgina ta rubuta da harshen Sifaniya, Ronaldo da Georgina Rodríguez sun hadu a shekarar 2016 a wani kantin sayar da kayayyaki na Gucci da ke birnin Madrid na kasar Sifaniya, inda Georgina ke aiki a wancan lokacin.
Sun fara soyayya ba da jimawa ba, inda suka fito fili suka bayyana alakar dake tsakaninsu a shekarar 2017, masoyan sun haifi yarsu ta farko, Alana, a watan Nuwamba na shekarar 2017, daga nan suka haifi tagwaye, Bella da Angel, a watan Afrilun 2022, amma jim kadan da haihuwarsu Angel ya rasu, Georgina ta kuma taimaka wajen renon wasu ‘ya’yan Ronaldo guda uku – Cristiano Jr., wanda aka haifa a watan Yuni 2010, da tagwaye Eva da Mateo wadanda aka haifa ta hanyar dashen kwayoyin halittta a watan Yunin 2017.
Ronaldo, mai shekaru 40, ya na cikin kakar wasa ta hudu tun bayan komawarsa kungiyar Al-Nassr ta kasar Saudi Arabia, tsohon dan wasan Real Madrid, Manchester United da Juventus ya lashe kyautar Ballon d’Or sau biyar, hakazalika, ya dauki kofin zakarun Turai biyar, ya kuma lashe gasar cin kofin nahiyar Turai da kasar Portugal a shekarar 2016.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp