Wasu ‘yan bindiga sun kai wani mummunan hari kan masallata a ƙauyen Marnona da ke ƙaramar hukumar Wurno ta jihar Sokoto, inda suka kashe wani mutum ɗaya tare da jikkata wasu da dama.
Wannan lamarin ya faru ne a lokacin da suke tsaka da sallah, lamarin ya kara bayyanar da matsalar tsaro a yankin gabashin Sokoto, wanda dama yake fama da matsalar tsaro a yankin.
- Xi: Sin Da Brazil Na Iya Zama Misalin Hadin Kai Da Dogaro Da Kai Ga Kasashe Masu Tasowa
- Ronaldo Zai Daura Aurensa Na Farko A Rayuwa Tare Da Budurwarsa Georgina
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa, maharan ɗauke da muggan makamai sun kutsa kai cikin masallacin da sanyin safiya, inda suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi a kan masallatan.
Harin ya matukar tayar da hankalin al’ummar yankin, inda mazauna wurin suka tsere domin tsira da rayukansu.
Rundunar ‘yansandan jihar Sokoto ba ta fitar da adadin waɗanda suka mutu ko suka ji rauni ko kuma aka sace su ba a yayin kai harin.
Shugaban jam’iyyar APC a jihar Sokoto, Honarabul Isah Sadeeq Achida, ya yi Allah wadai da faruwar lamarin, inda ya bayyana shi a matsayin harin dabbanci.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp