Rundunar ‘yansandan jihar Yobe ta cafke wani matashi mai suna Abdullahi Aliyu ɗan shekara 24, ɗan asalin garin Kakuri da ke jihar Kaduna bisa zargin yin garkuwa da wani ƙaramin yaro ɗan shekara 2 mai suna Abdulkareem Mohammed.
A ranar 31 ga watan Yulin 2025 ne dai aka sace Abdulkareem a garin Potiskum, inda Aliyu ya tuntuɓi mahaifin yaron, Mohammed Ishayaku domin ya biya kuɗin fansa naira miliyan biyu.
- ‘Yan Majalisa Na Ba Da Cin Hancin Har Naira Miliyan 3 Kafin Su Iya Gabatar Da Wani Ƙudiri – Kamfani.
- Sin Ta Kara Yawan Tallafinta Ga Hukumar Kula Da ‘Yan Gudun Hijirar Falasdinu
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar Yobe, SP Dungus Abdulkarim ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da LEADERSHIP ta samu a Damaturu, jihar Yobe.
Abdulkarim ya ce, ɗaukin gaggawar da ‘yansandan suka yi ne ya sa aka ceto yaron tare da cafke wanda ake zargin, Aliyu.
Rundunar ‘yansandan ta kara da cewa, an gano wanda ake zargin, kuma an kama shi a jihar Kaduna bayan bincike ya nuna cewa yana da hannu a irin wannan lamari a wasu jihohin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp