Ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) ta baiwa gwamnatin tarayya wa’adin kwanaki bakwai domin ta mayar da duk wasu kuɗaɗen ma’aikata da ake zargin an karkatar daga Asusun NSITF tare da gaggauta kafa hukumar gudanarwa ta Hukumar Fansho ta ƙasa (PENCOM). Ta gargadi cewa kin yin hakan zai jefa kasar cikin rikicin masana’antu.
A wata sanarwa da ta fitar bayan taron kwamitin aiki, wanda shugaban NLC, Kwamared Joe Ajaero ya sanya wa hannu, ƙungiyar ta zargi gwamnati da tauye haƙƙin ma’aikata da karya dokokin kare kuɗaɗen fansho da taimakon doreszamantakewa. NLC ta nuna fushi kan rahoton karkatar da kaso 40 na kuɗin gudunmawar ma’aikata na NSITF zuwa asusun gwamnati a matsayin kuɗin shiga, tana mai cewa hakan ya sabawa dokar kafa hukumar.
- Biyan ‘Yan Fansho Naira Biliyan 22: NUP Da NLC Sun Bukaci A Yi Koyi Da Gwamna Abba
- ‘Yan Nijeriya Ku Kauracewa Amfani Da Layukan Waya Na MTN, Airtel Da Glo – NLC
Kungiyar ta kuma yi Allah-wadai da yunƙurin gyara dokar NSITF domin baiwa gwamnati cikakken iko kan kuɗaɗen, tana mai gargadin cewa hakan zai tauye ikon ma’aikata kuma ya saɓa ƙa’idojin ƙwadago na ƙasa da ƙasa.
Haka kuma, NLC ta ce rashin kafa hukumar gudanarwa ta PENCOM ya haifar da giɓi a shugabanci, inda kuɗaɗen fansho ke ƙarƙashin ikon jami’an gwamnati kaɗai ba tare da wakilcin ma’aikata da masu ɗaukar ma’aikata ba.
Sanarwar ta ce dole ne a dawo da duk kuɗaɗen da aka karkatar cikin kwanaki bakwai tare da kafa shugabancin hukumar PENCOM bisa ƙa’ida, Idan ba a yi haka ba, NLC ba za ta sake bayar da tabbacin zaman lafiya a masana’antu ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp