Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) za ta gudanar da zaɓen cike gurbi a yau a faɗin Nijeriya domin cike guraben Majalisar Dokoki ta Ƙasa da na majalisun dokokin jihohi.
Zaɓukan za su gudana ne a jihohi 12, da suka shafi ƙananan hukumomi 32 da mazabu 356, a rumfunan zaɓe 6,987 gaba ɗaya. Hukumar ta ce jimillar masu kaɗa ƙuri’a a wuraren zaɓen sun kai mutum miliyan 3,553,659.
- INEC Ta Gargaɗi Ƴan Siyasa Kan Azarɓaɓin Yaƙin Neman Zaɓen 2027
- INEC Ta Ayyana 16 Ga Agusta Don Gudanar Da Zaben Cike Gurbi A Jihohi 12
Hukumar ta bayyana cewa dalilin gudanar da wannan zaɓen cike gurbi yana da nasaba ne da rasuwar wasu ‘yan majalisa, ko ajiye muƙami daga wasu, da kuma umarnin sake zaɓe da kotu ta bayar a wasu mazaɓun.
INEC ta yi kira ga al’umma da su halarci zaɓen cikin lumana, tare da bin ƙa’idojin zaɓe da tabbatar da cewa kowa ya sami damar kaɗa ƙuri’arsa cikin aminci.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp