Rasha ta yi kira ga kasashen duniya su hada karfi da karfe wajen taimakon hadakar kasashen Alliance of Sahel States wato AES domin ba su taimakon da suke bukata a yakin da suke yi da matsalar tsaro.
Kasashen AES din su ne Mali da Burkina Faso da kuma Nijar wadanda suke karkashin mulkin soja bayan shugabannin mulkin kasashen sun hambarar da gwamnatin fararen hula.
Kafar Actualite.bf mai zaman kanta ne ta ruwaito cewa Rasha ta gabatar da wannan kokon baran ne a jawabinta ga kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, inda wakilinta na dindindin, Dmitry Chumakob ya ce kasashen na bukatar agajin tsaro.
“Domin samun dawwamammen zaman lafiya, ya kamata kasashen duniya su ba kasashen Mali da Burkina Fasp da Nijar gudunmuwa,” in ji Chumakob.
Ya kara da cewa, “kasashen Afirka din ne da kansu suka fi sanin yadda za su magance matsalolin da suke fuskanta, kuma su ne suka fi sanin yadda za su yi yaki da matsalar tsaro da kuma hanyoyin inganta dimokuradiyya da tattalin arzikinsu.”
Rasha dai ta zama babbar kawar kasashen na AES, wadanda ke jan jikinsu daga wasu kasashen na yamma, inda Moscow ta kuduri aniyar taimakon kasashen wajen yaki da masu tayar da kayar baya.
Nijer Ta Ceto ‘Yan Gudun Hijira Da Suka Makale A Libya
Sojojin Jamhuriyar Nijar sun samu nasarar ceto ‘yancirani guda 50 da suke makala a sahara a hanyarsu ta tafiya kasar Libya.
RFI ta ruwaito cewa mutanen sun makale ne a kusa da bakin iyakar shiga kasar ta Libya bayan motarsu ta lalace a ranar 10 ga watan Agusta.
“Motarsu ta lalace ne a hanyarsu ta tafiya Libya, kasar da ake ratsawa domin tafiya kasashen turai. A ciki akwai fasinjoji 44 kuma motar tana tafiya ne a hanyar Madama-Dao da ke arewacin Nijar a lokacin da ta lalace, ta tsaya cak,” in ji rahoton na RFI.
Daga baya ne aka shiga neman motar, inda sojojin suka samu nasarar ceto su, sannan aka kai su garin Madama, inda ake cigaba da kula da su.
Sai dai har yanzu ba a tabbatar da asalin kasashen da mutanen suka fito ba, da kuma asalin kasar da suke shirin zuwa.
M23 Ta Musanta Zargin Kashe Gomman Fararen Hula A Kudancin Kibu
Kungiyar ‘yantawaye ta M23 a Congo ta musanta zarginta da ake yi da kashe gomman fararen hula a Kudancin Kibu na kasar, sannan kuma ta nanata cewa zarginta da ake yi da amfani da kananan yara a yaki kanzon kurege ne.
Kakakin M23, Willy Ngoma ne ya bayyana wa BBC haka, inda ya ce ko kadan ba ya cikin tsarinsu kai farmaki kan fararen hula.
“Ba ma kashe fararen hula. Ta yaya za mu kashe ‘yankasa, wadanda muke fafutikar karewa?
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp