A daren jiya Asabar, bisa agogon birnin Beijing, an yi gwaji na biyu game da ayyukan da za a gudanar da su, a bikin tunawa da cikar shekaru 80 da samun nasarar Sinawa a yaki da hare-haren Japan, da yakin da mutanen duniya suka yi don dakile zaluncin ‘yan mulkin danniya, da ake sa ran gudanar da shi a ranar 3 ga watan Satumba mai zuwa.
An ce mutane kimanin dubu 40 ne suka halarci gwajin da aka yi a wannan karo. Kana an tantance karin wasu ayyuka wajen gwajin da aka yi, misali yadda mutane za su taru a wajen bikin, kana ta yaya za su rabu zuwa wurare daban daban, da dai sauran su, wadanda duka kari ne idan an kwatanta da gwajin ayyukan da aka gudanar da shi a karon farko.
An ce sakamakon gwajin ya nuna cewa, shirin da aka yi yana da inganci, kana an kara tabbatar da gudanar ayyukan ba da jagoranci da tsare-tsaren harkoki yadda ake bukata. A nasu bangaren, hukumomin birnin Beijing sun nuna godiya ga jama’a mazauna birnin, bisa yadda suka goyi bayan ayyukan da aka gudanar, wadanda suka shafi wasu bangarorin birnin. (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp