ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, July 13, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

DSS Ta Gurfanar Da Shugabannin Ƙungiyar Ansaru Kan Zargin Ta’addanci

by Sadiq
10 months ago
DSS

Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta gurfanar da manyan shugabannin ƙungiyar ta’addanci ta Ansaru, a gaban Kotun Ƙoli ta Tarayya da ke Abuja a ranar Laraba.

Mutanen su ne Mahmud Usman (wanda ake kira Abu Bara’a Abbas ko Mukhtar) da mataimakinsa, Mahmud Al-Nigeri (wanda aka fi sani da Malam Mamuda).

  • ‘Yansanda Sun Cafke ‘Yan Fashi 3 A Kano, Sun Ƙwato Motar Sata
  • Amfani Da Karfin Tuwo Ba Zai Iya Kawo Zaman Lafiya A Yankin Gabas Ta Tsakiya Ba

Ana tuhumar su da zarge-zarge 32 da suka shafi ta’addanci a gaban Mai Shari’a Emeka Nwite.

ADVERTISEMENT

DSS ta ce waɗannan mutane ne suka kai harin gidan yarin Kuje a watan Yulin 2022, wanda ya bai wa fursunoni sama da 600 damar tserewa.

Haka kuma, ana tuhumar su da kitsa kai harin sansanin sojin Nijeriya na Wawa a Jihar Neja a 2022, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.

LABARAI MASU NASABA

Mahara Sun Kashe Mutane 9 Ƴan Gida Ɗaya, Har Da Jariri Ɗan Wata 2 A Filato

Hukumar Alhazai Ta Kano Ta Sa Miliyan 8.5 A Matsayin Kuɗin Hajjin 2027

DSS ta ce, shugabannin sun samu horo na musamman a kan amfani da makamai, dabarun yaƙi da kuma ƙera bama-bamai a ƙasashen Mali da Libya.

Ta ce Mamuda ya samu horo na musamman daga malamai masu tsattsauran ra’ayi a tsakanin 2013 da 2015.

Hakazalika, suna da hannu a sace manyan mutane, ciki har da sace wani Injiniya ɗan ƙasar Faransa, Francis Collomp a 2013 da kuma sace Alhaji Musa Umar Uba, Magajin Garin Daura a 2019.

Ana kuma zarginsu da fashi da makami da kuma shirin kai hari wajen wani haƙar uranium a Nijar, wanda shirin nasu bai yi nasara ba.

Mai Bai wa Shawara kan Sha’anin Tsaro, Nuhu Ribadu ne, ya tabbatar da kama su yayin wani samamen haɗin gwiwa da jami’an tsaro suka kai.

Ribadu ya ce kama su zai kawo wa shugabancin ƙungiyar ta Ansaru koma baya.

Ansaru ta ɓalle daga cikin Boko Haram a 2012, inda da farko ta bayyana kanta a matsayin ƙungiya mai “tausaya wa al’umma.”

Amma daga baya ta haɗu da ƙungiyoyin ta’addanci na ƙasa da ƙasa, har ta ɗauki tambarin Al-Qaeda.

MASU ALAKA

Mahara Sun Kashe Mutane 9 Ƴan Gida Ɗaya, Har Da Jariri Ɗan Wata 2 A Filato
Manyan Labarai

Mahara Sun Kashe Mutane 9 Ƴan Gida Ɗaya, Har Da Jariri Ɗan Wata 2 A Filato

July 12, 2026
Hukumar Alhazai Ta Kano Ta Sa Miliyan 8.5 A Matsayin Kuɗin Hajjin 2027
Manyan Labarai

Hukumar Alhazai Ta Kano Ta Sa Miliyan 8.5 A Matsayin Kuɗin Hajjin 2027

July 12, 2026
An Kashe Fitaccen Kwamandan ’Yan Bindiga, Kachalla Sani Yellow A Zamfara
Manyan Labarai

An Kashe Fitaccen Kwamandan ’Yan Bindiga, Kachalla Sani Yellow A Zamfara

July 12, 2026
Next Post
‘Yan Bindiga Sun Sace Mutum 7 A Jihar Neja

Cutar Diphtheria Ta Kashe Yara 10 A Jihar Neja

LABARAI MASU NASABA

Sin Tana Matsayi Na Farko A Duniya A Fannin Kirkire-kirkiren Wutar Lantarki

Sin Tana Matsayi Na Farko A Duniya A Fannin Kirkire-kirkiren Wutar Lantarki

July 12, 2026
Mahara Sun Kashe Mutane 9 Ƴan Gida Ɗaya, Har Da Jariri Ɗan Wata 2 A Filato

Mahara Sun Kashe Mutane 9 Ƴan Gida Ɗaya, Har Da Jariri Ɗan Wata 2 A Filato

July 12, 2026
Sin Ta Yi Kunnen Doki Da Nijeriya A Gasar Kwallon Kafa Tsakanin Kasashe 4 Ta ‘Yan Kasa Da 17

Sin Ta Yi Kunnen Doki Da Nijeriya A Gasar Kwallon Kafa Tsakanin Kasashe 4 Ta ‘Yan Kasa Da 17

July 12, 2026
FIFA Na Nazarin Faɗaɗa Gasar Kofin Duniya Zuwa Ƙasashe 64

FIFA Na Nazarin Faɗaɗa Gasar Kofin Duniya Zuwa Ƙasashe 64

July 12, 2026
Hukumar Alhazai Ta Kano Ta Sa Miliyan 8.5 A Matsayin Kuɗin Hajjin 2027

Hukumar Alhazai Ta Kano Ta Sa Miliyan 8.5 A Matsayin Kuɗin Hajjin 2027

July 12, 2026
Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin Ta Fitar Da Sanarwa Game Da Cika Shekaru 10 Da Fitar Da Hukuncin Takkadamar “Philippines Da China”

Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin Ta Fitar Da Sanarwa Game Da Cika Shekaru 10 Da Fitar Da Hukuncin Takkadamar “Philippines Da China”

July 12, 2026
Atiku Ya Soki Shirin Ƙara Kuɗin Jarabawar WAEC Da NECO Zuwa N50,000

Atiku Ya Soki Shirin Ƙara Kuɗin Jarabawar WAEC Da NECO Zuwa N50,000

July 12, 2026
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya

Daraktan Hollywood Carl Rinsch Zai Shafe Watanni 30 A Gidan Gyaran Hali

July 12, 2026
Mataimakin Firaministan Sin Ya Jadadda Bukatar Kare Rayuka Da Dukiyoyin Jama’a Yayin Rangadi A Beijing

Mataimakin Firaministan Sin Ya Jadadda Bukatar Kare Rayuka Da Dukiyoyin Jama’a Yayin Rangadi A Beijing

July 12, 2026
Tarihin Sarakunan Da Suka Yi Wa Turawan Mulkin Mallaka Turjiya A Nijeriya

Tarihin Sarakunan Da Suka Yi Wa Turawan Mulkin Mallaka Turjiya A Nijeriya

July 12, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.