Alkaluman da aka samu a shafin yanar gizo na harkokin fina-finan kasar Sin sun nuna cewa, fim da ake nunawa mai taken “Tabbatattun Shaidu”, ko kuma “Dead To Rights” a Turance, na samun karbuwa sosai tsakanin al’ummun kasar, inda bayan wasu kwanaki 23 da aka kwashe ana haska fim din, yawan kudin da aka samu bisa sayar da tikitin kallo ya zarce kudin Sin Yuan biliyan 2.5, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 348.
An tsara fim din ne bisa tarihin kisan kiyashin da sojojin kasar Japan suka yi a birnin Nanjing, fadar mulkin kasar Sin a lokacin, a karshen shekarar 1937 zuwa farkon shekarar 1938, inda maharan Japan suka kashe Sinawa kimanin dubu 300 a birnin.
Cikin fim din mai taken “Tabbatattun Shaidu”, an bayyana labarin da ya shafi yadda dimbin jama’ar birnin Nanjing suka sadaukar da ransu don kare wasu hotuna, wadanda suka kasance shaidun ta’asar da Japanawa suka aikata a Nanjing.
Bana shekara ce ta cika shekaru 80 da samun nasarar yakin da Sinawa suka yi da mahara Japanawa, da yakin da mutanen duniya suka yi don dakile zaluncin mulkin danniya. Sakamakon haka, ana ta nuna wasu fina-finai, da wasannin kwaikwayo, da kide-kide, da bukukuwan rawa, masu alaka da tarihin yakin, a kasar ta Sin. (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp