Pan Chunlin, mai hakar ma’adinai a kauyen Yucun, wani karamin kauye a lardin Zhejiang dake kasar Sin, ba zai taba mantawa da wani lokaci da gari ya yi masa zafi ba a shekaru 20 da suka gabata. Lokacin da aka rufe dutsen ma’adanai a watan Agustan 2005, ya bar aikin hakar ma’adanai da yake samun kudin shiga kusan yuan miliyan daya a ko wace shekara. Bai taba tunanin cewa bayan shekaru 20, otel da yake gudanarwa wanda tsaunuka masu shuke-shuke suka kewaya, zai samar da kudin shiga na kusan yuan miliyan hudu a duk shekara ba, kuma har ma za a sanya wa kauyen Yucun suna “Kauyen yawon bude ido tamkar aljannar duniya.”
An fara wannan sauyi ne a shekaru 20 da suka gabata, lokacin da Xi Jinping, wanda a lokacin yake kula da harkokin lardin Zhejiang, ya bayyana cewa, “Muhallin hallitu shi ne dukiya,” wato manufa ce ta raya kasa ta hanyar bayar da muhimmnci ga “Muhalli”. Wannan bayani mai cike da hikima, a hankali ya zama “juyin juya hali mai kiyaye muhalli” wanda ya kawo sauyi a kasar Sin kuma ya yi tasiri a duniya.(Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp