Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya jaddada muhimmancin kara zage damtse, wajen karfafa farfadowar tattalin arzikin kasar, da shigar da karin kuzari cikin ayyukan samar da ci gaba, kana da azamar kammala muradun bunkasa tattalin arziki da zamantakewar al’ummar kasar na bana.
Li Qiang, ya bayyana hakan ne a jiya Litinin, yayin da yake jagorantar zama na tara na majalissar zartarwar kasar Sin, yana mai cewa wajibi ne a inganta matakan aiwatar da manufofin raya tattalin arziki daga manyan fannoni, da mayar da hankali ga muhimman fannoni da ake baiwa fifiko, ta yadda za a karfafa tattalin arzikin cikin gida, da cimma gajiyar daidaito da ci gaba na dogon lokaci, don sassauta tasirin rashin tabbas da ake iya gamuwa da shi daga huldar kasa da kasa.
- Zaɓen Cike Gurbi: ‘Yansanda Sun Gurfanar Da Mutane 333 Da Ake Zargi Da Aikata Laifuka A Kano
- Akpabio Ya Ƙaryata Jita-jitar Ba Shi Da Lafiya
Daga nan sai firaministan na Sin ya yi kira da a ci gaba da ingiza matakan sayayya, da kawar da shingaye masu tarnaki ga fannin, da kara ingiza sabbin ginshikan samar da ci gaba, da suka hada da na sayayyar hidimomi da sauran sabbin fannonin sayayya.
Kazalika, Li Qiang ya yi kira da a zurfafa dunkule fannonin kirkire-kirkiren kimiyya da na masana’antu, da kara bunkasa bude kofa mai matukar inganci. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp