Rundunar ‘yansandan jihar Kaduna ta kama wasu mutane 13 da ake zargin ɓarayin shanu ne tare da kwato shanu 27 a wani gagarumin ci gaba na yaki da ‘yan bindiga a jihar.
An kama mutanen ne a ranar Lahadi, 17 ga watan Agusta, 2025, biyo bayan sahihan bayanan sirri da jami’in ‘yansanda (DPO) na Toll Gate Division ya samu.
Da gaggawa DPO din ya tattara tawagar jami’an tsaro tare da kafa wani shingen bincike akan hanyar Kaduna zuwa Abuja.
A cewar wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a (PPRO) na rundunar ‘yansandan (PPRO) jihar, DSP Mansir Hassan, ya fitar, ya ce, binciken ya yi sanadin kwato motoci uku da ke jigilar shanun da aka sace.
A cewar PPRO, sauran wadanda aka kama a wurin sun hada da Lawal Sarki, Sule VIO, Ayuba Mohammed, Mohammed Bashir, Abu Mai Chaji, Abdullateef Lateef, Shamsudden Abdullahi, Jonathan Ishaya, da Yakubu Alhassan. Daga baya kuma an kara kama wasu da suka hada da Alh. Abu, Lawal Abdullahi, Shamsudeen Abdullahi, da Abba Hamisu.














