Zuwa karshen 2024, jimilar wuraren wasanni da motsa jiki dake fadin kasar Sin ya kai murabba’in mita biliyan 4.23, karuwar muraba’in mita biliyan 1.131, idan aka kwatanta da karshen shekarar 2020. Daraktan hukumar kula da wasanni ta kasar Sin Gao Zhidan ne ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai da aka yi yau Talata, inda ya kara da cewa, adadin masu motsa jiki a-kai-a-kai ya zarce kaso 38.5 cikin dari.
Taron ya kuma bayyana nasarorin da Sin ta samu na zama mai karfi a bangaren wasanni a wa’adin shirin raya kasa na shekaru 5 na 14, tsakanin 2021 zuwa 2025.
Gao Zhidan ya kara da cewa, zuwa karshen shekarar 2024, ’yan wasan guje-guje da tsalle-tsalle na kasar Sin, sun lashe gasanni 519 na duniya tare da kafa tarihi a bangarori 68. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp