Kungiyar kwallon kafa ta AC Milan dake buga gasar Serie A ta kasar Italiya ta fara tattaunawa da Bayern Leverkusen yayin da ta ke neman daukar dan wasan gaban tawagar Nijeriya Victor Boniface, masanin harkokin kwallon kafa Fabrizio Romano ne ya bayyana haka a shafinsa na X.
Romano ya rubuta “Milan da Bayern Leverkusen suna ci gaba da tattaunawa kan yarjejeniyar daukar Victor Boniface, tattaunawa tana gudana a yau (Laraba) kuma ga alama Victor ya bayyana amincewa dangane da zuwa Milan, yanzu haka daukar dan wasan na Nijeriya na daga cikin abubuwan da kocin Milan Massimiliano Allegri ya bai wa fifiko.
Bayan tattaunawa da wakilan Boniface, dan wasan mai shekaru 24 ya ba da tabbacin amincewa da komawa Milan kuma akwai yiwuwar kammala yarjejeniyar cikin lokaci kadan mai zuwa, yanzu Milan ta tuntubi Leverkusen domin cimma yarjejeniyar kudi domin daukar Boniface.
Wannan na zuwa ne wata guda bayan wata hira da Boniface ya yi da jaridar SportBild, inda ya bayyana cikakkiyar sadaukarwa ga Bayern Leverkusen, LEADERSHIP ta fahimci cewa Boniface yanzu ya nuna sha’awar barin Jamus kuma ya zama wani muhimmin bangare na shirye-shiryen Milan a kakar wasa ta bana.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp