Gwamnatin Amurka ta bayyana damuwarta kan dorewar sabon mafi karancin albashin Nijeriya, inda ta yi gargadin cewa ma’aunin na ₦70,000 da aka amince da shi a baya-bayan nan bai isa ya fitar da ‘yan kasar daga kangin talauci ba saboda tabarbarewar tattalin arzikin kasar.
A cikin rahotonta na kasa na 2024 kan ayyukan kare hakkin bil’adama, wanda Ofishin Jakadancin Amurka na Ofishin Dimokuradiyya, Kare Hakkokin Dan Adam da kwadago, ya fitar a ranar 12 ga Agusta, 2025, Washington ta yi nuni da cewa, mafi karancin albashi, wanda a halin yanzu ya kai kusan dala 47.90 a kowane wata a kan farashin canji akan N1,500 na dala, yanzu ya ci gaba saboda faduwar darajar Naira.
- Ac Milan Na Tattaunawa Da Bayern Leverkusen Akan Yunkurin Daukar Boniface
- Za A Shigar Da Karin Makudan Kudade Domin Ayyukan Kyautata Rayuwar Al’ummun Jihar Xizang Ta Kasar Sin
Rahoton ya lura cewa, duk da cewa dokar ta 2024 (wacce aka yi wa kwaskwarima) ta mafi ƙarancin albashin ma’aikata, ta ninka inda ta baro a baya, amma aiwatar da ita ya zama babban kalubale a duk faɗin ƙasar.
Ya kara da cewa gwamnatin Nijeriya ba kasafai take tabbatar da bin doka ba, yayin da wasu jihohi suka ki aiwatar da dokar, saboda matsalar kudi.
“Kamfanoni da yawa suna da kasa da ma’aikata 25, kuma wannan doka ta fadi a kansu,” in ji rahoton, yana mai jaddada cewa dokar ta shafi kamfanoni ne da ke da ma’aikata 25 ko fiye da haka.
Ya kuma kara da cewa, ma’aikatan aikin gona da ma’aikatan wucin gadi, da wadanda ke kan aikin kwangiloli, su ma wannan dokar ta fadi a kansu.
Rahoton ya kuma ce, tsakanin kashi 70 zuwa 80 cikin 100 na ma’aikatan Nijeriya na aiki ne a karkashin kansu, suma haka, wannan doka ta fadi a kansu.
Bisa kididdigar da Amurka ta yi, yawan masu sa ido kan ayyukan kwadago a kasar bai isa ba wajen sa ido kan yadda ake bin doka da oda, lamarin da ya sa miliyoyin ma’aikata ke fuskantar cin zarafi.
Wannan tantancewar dai na zuwa ne a daidai lokacin da Nijeriya ke ci gaba da samun sauye-sauyen tattalin arziki da suka hada da batun cire tallafin man fetur da kuma hada-hadar canjin kudi, wadanda suka haifar da hauhawar farashin kayayyaki da kuma tabarbarewar tsadar rayuwa ga talakawan Nijeriya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp