Yau Alhamis, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin, Mao Ning ta gudanar da taron manema labarai na yau da kullum.
Dangane da batun jiragen ruwan yakin Amurka da ke sintiri a gabar tekun Caribbean da kuma yiwuwar yin amfani da karfin tuwo kan kasar Venezuela bisa hujjar yaki da miyagun kwayoyi, Mao Ning ta bayyana cewa, kasar Sin na adawa da amfani ko barazanar karfin tuwo a cikin huldar kasa da kasa da kuma tsoma bakin waje cikin harkokin cikin gidan Venezuela a kan ko wane dalili. Kasar Sin na fatan Amurka za ta kara yin kokari wajen inganta zaman lafiya da tsaro a yankin Latin Amurka da Caribbean.
Dangane da wasu takardu na Rasha da aka fallasa da ke bayyana laifukan yakin amfani da hallitu masu haddasa cututtuka da Japan ta yi, Mao Ning ta yi bayanin cewa, bayanan da gwamnatin Rasha ta fitar sun sake nuna hujjojin da ba za a iya canzawa ba na laifukan sojojin Japan na aikata yakin amfani halittu masu cutarwa, wadanda ba za a iya karyatawa ba.
Dangane da ci gaban da ingantaccen cinikin waje na kasar Sin ke samu kuwa, Mao Ning ta bayyana cewa, kayayyakin da kasar Sin ke samarwa masu inganci sun shahara a duk duniya, kuma wannan abu ne da yakin haraji da yakin ciniki ba za su iya sauyawa ba.(Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp