An gudanar da taron kara wa juna sani kan kare hakkin bil’adama na Sin da Afirka karo na farko a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, jiya Jumma’a bisa taken “Gina al’ummar Sin da Afirka mai kyakkyawar makoma da yin aiki tare don tabbatar da ‘yancin samun ci gaba.”
Taron ya samu halartar masu tsara manufofi, da masana, da jami’an diflomasiyya, da wakilan kafofin watsa labarai na kasashen Sin da Afirka fiye da 200, domin lalubo hanyoyin da za a bi wajen karfafa hakkin dan Adam, musamman a bangaren ‘yancin samun ci gaba.
A jawabinsa a wajen taron, mataimakin shugaban kungiyar nazarin hakkin dan Adam ta kasar Sin Jiang Jianguo, ya bayyana cewa, ci gaba shi ne madawwamin jigon rayuwar bil’adama, kuma shi ne babban fifikon da jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ta sa gaba wajen gudanar da mulki.
A nasa bangaren, babban darektan cibiyar nazarin manufofi ta kasar Habasha, Fekadu Tsega, ya bayyana cewa, wannan taron na kara wa juna sani zai taimaka wajen inganta gina al’ummar Sin da Afirka mai kyakkyawar makoma guda, da taimaka wa tabbatar da ‘yancin samun ci gaba, yana mai bayyana taron a matsayin wani muhimmin dandali na kyautata tsara makomar gudanar da harkokin kare hakkin bil’adama, da kuma karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen Afirka da Sin. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp