Sakamakon kuri’un jin ra’ayin jama’a na baya bayan nan da kafar CGTN ta fitar, ya nuna gamsuwar jama’a da tasiri, da gudummawar Sin ga ci gaban kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai ko SCO.
Cikin masu bayyana ra’ayoyi 8,873 daga kasashen duniya 38 na kasashe masu tasowa, da masu samun saurin ci gaba, kaso 75.1 bisa dari na ganin Sin ta yi rawar gani wajen ingiza ci gaban kungiyar SCO. Kuma karkashin tsare-tsaren ayyukan SCO, adadin cinikayya tsakanin Sin da kasashe membobin kungiyar ya karu matuka cikin sama da shekaru 10, musamman kasashen tsakiyar Asiya. Kazalika, kaso 84.5 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyin sun amince SCO ta bayar da gudummawa mai kyau a fannin bunkasa tattalin arzikin kasashe membobinta.
A daya bangaren, kaso 86.8 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyin sun amince da ruhin “Shanghai”, wato mutunta juna, da cimma moriyar juna, da daidaito, da gudanar da shawarwari, da martaba mabanbantan wayewar kai, da samun ci gaban bai daya, sun kuma yarda da ingancin manyan ginshikan hadin kan kungiyar, wato kauracewa danniya, da salon fito na fito a fannin jagorancin shiyya, a duniya mai kunshe da mabanbantan tasiri. Yayin da kaso 69.3 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyin ke ganin SCO na da matukar tasiri a fannin jagorancin duniya musamman tsakanin kasashe membobinta. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp