Gwamnatin jihar Kano ta musanta zargin cewa babban daraktan kula da harkokin gidan gwamnati, Abdullahi Ibrahim Rogo ya karkatar da naira biliyan 6.5 daga asusun jihar, inda ta bayyana ikirarin a matsayin siyasa.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, zargin da wata jarida ta intanet ta rahoto a ranar 22 ga watan Agusta, ta bayyana cewa, Rogo ya cire kudaden ne tsakanin watan Nuwamba 2023 zuwa Fabrairu 2025 ta hannun kamfanoni, H&M Construction Nigeria Ltd, A.Y. Maikifi Petroleum, da kuma Ammas Oil and Gas Ltd.
- Beijing Zai Bunkasa Amfani Da Fasahohin Zamani A Wuraren Adana Kayan Tarihi
- Gwamnatin Sokoto Ta Ƙaryata Rahoton NBS Kan Talauci, Ta Ƙaddamar Da Sabon Bincike
A cewar jaridar, an karkatar da kudaden ne ta hanyar wasu kwangiloli da ba a aiwatar da su ba.
Amma, a cikin wata sanarwa mai kakkausar murya da ya fitar a ranar Litinin, Daraktan Yada Labarai na Gidan Gwamnati, Sanusi Bature DawakinTofa, ya karya rahoton da cewa “aiki ne na tatsuniyoyi, wadanda abokan hamayyar siyasa suka shirya su, domin bata wa gwamnati suna don su samu madafun iko gabanin zaben 2027.
“Kowane tsabar kudi da ke fita a cikin Ma’aikatun gwamnati a tsare suke yadda ya kamata a cikin kundin kasafin kudi na jihar. Don haka, babu wani mutum a cikin gwamnati da ke kula da kudaden jama’a ba tare da wata manufa ta musamman ba,” in ji sanarwar.














