Shugaban Kongo Brazzaville Denis Sassou Nguesso, ya bayyana a jiya Litinin 25 ga watan nan cewa, zai himmatu wajen sauke nauyin dake wuyan kasarsa, kasancewarta mai shugabancin hadin gwiwa na taron FOCAC, da kuma ingiza tabbatar da sakamakon taron Beijing cikin sauri.
Sassou Nguesso ya bayyana hakan ne yayin ganawa da An Qing, jakadiyar Sin dake kasarsa. Ya ce, bayan shekaru 60 da kafa huldar diflomasiyya tsakanin kasarsa da Sin, kasashen biyu sun ci gaba da kasancewa abokai na kut da kut. Ya kuma shaida bunkasar huldar kasashen biyu. Ya ce Kongo Brazzaville na shirin kara habaka huldar abota da Sin, da kuma kara zurfafa hadin gwiwa, don inganta dangantakarsu da ma tsakanin kasashen Afrika da Sin.
A nata bangare, An Qing ta ce, a karkashin jagorancin shugabannin kasashen biyu, Sin da Kongo Brazzaville sun karfafa amincewa da juna, suna tallafa wa juna, kuma suna samun ci gaba tare. Kazalika, dangantakar kasashen biyu ta zama misali ga hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa. Kuma Sin na shirin kara karfafa abota ta gargajiya da kasar, da tabbatar da amincin siyasa, da kuma zurfafa hadin gwiwa a fannoni daban-daban. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp