Wani nazari da kafar CGTN ta kasar Sin ta gudanar, wanda ya shafi mutane 11,913 daga kasashe sama da 40 ya nuna cewa, kaso 62.1 na mutane a fadin duniya sun yi imanin cewa, kare sakamakon yakin duniya na II abu ne mai matukar muhimmanci wajen tabbatar da odar duniya, inda kimanin kaso 58 daga cikinsu, suka ce odar duniya na tabarbarewa kuma kai tsaye sun bayyana Amurka a matsayin babbar mai haifar da tsaiko a duniya.
Yakin duniya na II wani mummunan lamari ne da dan adam bai taba ganin irinsa ba a tarihi. Kuma shekarun da aka shafe ana gwabzawa da mace-mace da asarar da yakin ya haifar da sadaukarwar da aka yi, dukkansu darasi ne da duniya za ta iya dauka don kaucewa maimaituwar yakin.
Idan zan ba da misali da kasar Sin, la’akari da yadda ta shafe tsawon shekaru 14 tana yaki da Japanawa masu kutse da asarar rayuka miliyan 35, kwatankwacin kaso 1 bisa 3 na jimilar asarar rayukan da aka yi a lokacin, za mu iya cewa ta fi kowa jin jiki yayin yakin, amma kuma ta yi nasara wajen yaki da mulkin danniya da kokarin wanzar da zaman lafiya a duniya. Ta kuma shiga an dama da ita wajen tsara yanayin tafiyar da harkokin duniya cikin lumana kuma bisa doka da adalci, tare da kai wa ga kafa MDD.
Sai dai duk da irin wannan sadaukarwa da aka yi, a halin da ake ciki yanzu, wasu ’yan tsiraru suna kokarin lalata ginshinkin zaman lafiyar duniya da haifar da rarrabuwar kawuna da ingiza rikici tsakanin kasa da kasa ta hanyar yada jita-jita da karairayi da fatali da dokokin kasa da kasa, domin cimma wasu burikansu.
Shin halin ni ’ya su da duniya ta shiga a wancan lokaci bai isa ya zama izina a gare su?
Yakin duniya na II abu ne da ya keta kasashe da iyakoki da launin fata, wanda a karshe ya kawo hadin kai tsakanin kasa da kasa domin wanzar da zaman lafiya da ci gaban duniya. Shekaru 80 bayan samun nasarar yaki da masu danniya, ya kamata a yi waiwaye, a nazarci nasarar da aka samu da kyar, da tsamo hikimomi da dabaru da ma hanyoyin karfafa gina duniya cikin kawanciyar hankali da lumana. Yayin da al’ummomin kasashen duniya ke ganin wasu kasashe na kokarin lalata wannan nasara, ya zama wajibi a tsaya tsayin daka wajen bijire musu, don ganin ba a bar su sun mayar da hannun agogo baya ba. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp