Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da aikin gyaran na’urar tiransimita mai gajeren zango (shortwave) ta gidan rediyon Muryar Nijeriya (VON) mai ƙarfin kilowat 250 TX2 a tashar da ke unguwar Lugbe a Abuja.
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, wanda Babban Sakatare a ma’aikatar, Mista Ogbodo Chinasa Nnam ya wakilta, shi ne ya bayyana hakan a bikin ƙaddamar wanda aka yi a ranar Talata a Abuja.
- Gwamna Buni Ya Kaddamar Da Dashen Bishiyoyi Na 2025
- Jami’an Tsaro Sun Ceto Mutane 128 Daga Hannun ‘Yan Bindiga A Zamfara
Idris ya bayyana wannan mataki a matsayin wani “muhimmin lokaci a tarihin Muryar Nijeriya, domin mun fara aikin farfaɗo da tasha mafi girma kuma mafi ƙarfi a nahiyar Afrika wadda yanzu ake sanya mata ingantattun na’urori na zamani da suka dace da fasahar zamani.”
Idris ya gode wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa hangen nesan sa da jajircewar sa wajen zamanantar da kayan aikin yaɗa labarai a Nijeriya.
A cewar sa: “Yayin da muke ɗaukar wannan babban mataki na ƙaddamar kwangilar gyara tiransimitar ‘shortwave’ ta Muryar Nijeriya mai ƙarfin kilowat 250, ya dace mu nuna ɗimbin godiyar mu ga Mai Girma Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, GCFR, bisa hangen nesa da jajircewar sa wajen farfaɗo da kuma zamanantar da kayan aikin yaɗa labarai na Muryar Nijeriya.”
Ya kuma tabbatar wa da ‘yan Nijeriya cewa wannan aikin zai sauya yanayin yadda ake yaɗa labarai a ƙasar nan.
Ya ce: “Da zarar an kammala wannan aiki, na’urorin tiransimita na VON da aka farfaɗo da su gaba ɗaya za su sauya yanayin yaɗa shirye-shiryen rediyo na ƙasa, tare da sanya VON a matsayin gagarumar alama mai martaba a duniyar yaɗa labarai ta rediyo baki ɗaya.”
Ministan ya buƙaci kamfanin Confax Nigeria Limited da ke gudanar da kwangilar da ya tabbatar da inganci da kuma kammalawa a kan lokaci, inda ya ce: “Saboda haka ina kira ga ɗan kwangilar da ya tabbatar da ba wai kawai an kammala aikin a cikin lokacin da aka tsara ba, har ma a tabbatar da cewa an kiyaye mafi girman matakan inganci kuma hakan ya fito fili.”
Haka kuma ya umurci ma’aikatan da ke kula da na’urori a VON da su yi aiki da jajircewa da natsuwa wajen kula da wannan aikin.
Ya jaddada cewa ana sa ran gidan rediyon VON zai ci gaba da kiyaye manufar sa ta kasancewa gidan rediyo mai goyon bayan Nijeriya da Afrika baki ɗaya, tare da bayar da sahihan labarai na nasarorin da ke fitowa daga Nijeriya da nahiyar baki ɗaya.
A ƙarshe, Ministan ya ce: “Yanzu ina farin cikin ƙaddamar da kwangilar gyaran na’urar tiransimitar ‘shortwave’ ta Muryar Nijeriya mai ƙarfin kilowat 250.”
Shi dai VON, shi ne gidan rediyon da Gwamnatin Tarayya ta kafa domin bada labarai daga Nijeriya zuwa ƙasashen ƙetare, kwatankwacin gidan rediyon BBC da na Muryar Amurka.
An kafa shi a cikin 1961 a matsayin sashen labaran ƙetare na gidan rediyon NBC, wato wanda ya zama FRCN daga bisani. Firayim Minista na lokacin, Alhaji Sa Abubakar Tafawa Balewa, shi ne ya ƙaddamar da shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp