A yau da safe, cibiyar manema labarai ta bikin cika shekaru 80 da cimma nasarar yaki da maharan Japan da yakin tafarkin murdiyya na duniya, ta gudanar da taron manema labarai karo na biyu, inda aka yi karin haske game da ci gaba cikin kwanciyar hankali da inganta ra’ayin gina kyakkyawar makomar bil adam ta bai daya da aka samu, tare da amsa tambayoyin ‘yan jarida.
Mataimakin ministan harkokin wajen Sin Ma Zhaoxu ya bayyana cewa, ra’ayin kafa kyakkyawar makomar bil adam ta bai daya ya sauya daga wata shawara ta Sin zuwa ra’ayin bai daya da ya samu amincewar duniya, kuma daga kyakkyawan fata zuwa aiki mai fa’ida, kazalika daga ra’ayi zuwa tsarin kimiyya, inda aka samu nasarori masu yawa a mabambantan bangarori.
Ya ce, al’ummar duniya sun yarda cewa wannan shawara tana nuna hangen nesa irin na Sin game da ci gaban dan adam, kuma tana da muhimmin tasiri wajen hada kan kasashe don samar da kyakkyawar makoma ga duniya. Har ila yau, an dauki shekaru 8 a jere ana rubuta wannan babban ra’ayi cikin kudurin MDD, kuma an sanya shi cikin sanarwar taron shugabannin kungiyar hadin kai ta Shanghai (SCO) sau 8. Haka kuma, ya shiga cikin sanarwar taron shugabannin kasashen BRICS, an kuma sanya ainihin ma’anarsa cikin yarjejeniyar nan ta “Future Pact” mai nufin samar da kyakkyawar makoma ga zuri’a ta gaba.
Haka kuma, Ma Zhaoxu ya bayyana cewa, kasar Sin tana son mutunta juna, da zaman tare cikin lumana, da kulla hadin gwiwar samun nasara ga kowane bangare tare da Amurka, bisa tabbatar da kare muradun ikon mallakar yankunan kasarta, da tsaro da kuma ci gaban kasar.
Ya kara da cewa, a shirye muke mu yi aiki tare da Amurka a kan turba guda, da aiwatar da muhimman yarjejeniyoyi da shugabannin kasashen biyu suka cimma, da ci gaba da sadarwa a tsakaninmu, da warware batutuwan da muka sha bamban a kai, da fadada hadin gwiwa, da kuma ci gaba da lalubo hanyar da ta dace manyan kasashen biyu su tafi tare da juna a sabon zamani.
Jami’in ya kuma yi nuni da cewa, batun yankin Taiwan ya kasance jigo a cikin muradun kasar Sin. Kana lamarin yankin na Taiwan sha’ani ne na cikin gidan kasar Sin, kuma ba a yarda da shisshigin kasashen waje ba. Haka nan, ba za a taba iya dakatar da burin da aka sa gaba na cewa tabbas wata rana za a wayi gari kasar Sin ta dunkule wuri guda ba. (Mai Fassara: Amina Xu, Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp