Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ce har kullum kasar Sin za ta kasance amintacciyar abokiyar huldar MDD, kuma a shirye take ta zurfafa hadin gwiwa da majalisar, da tallafa mata, ta yadda MDDr za ta taka muhimmiyar rawar jagoranci a harkokin kasa da kasa, da hada karfi da karfe wajen sauke nauyin dake wuyanta na kare yanayin zaman lafiyar duniya, da ingiza ci gaba da walwalar dukkanin sassa.
Shugaba Xi, ya bayyana hakan ne a Asabar din nan, yayin da yake ganawa da babban magatakardar MDD Antonio Guterres, a birnin tashar ruwa na Tianjin. Ya ce tarihi ya nuna yadda cudanyar mabambantan sassa, da goyon baya da hadin gwiwa, suka kasance amsa ga tarin kalubalen dake addabar duniya.
Mista Guterres, ya isa birnin Tianjin ne domin halartar taron koli na kungiyar hadin kai ta Shanghai ko SCO na shekarar nan ta 2025. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp