Sufeton Janar na ‘yansandan Nijeriya, Usman Baba, ya yi gargadi da kakkausar murya tare da yin Allah wadai da kai hare-hare wa jami’an ‘yansanda a yayin da suke bakin aiki a sassa daban-daban na kasar nan.
Ya ce ‘yansandan da ke sanye da uniform din aiki suna aiki ne da kare doka da oda don haka farmakarsu babban kuskure ne.
Kamar yadda Kakakin hukumar CSP Olumuyiwa Adejobi ya nakalto, shugaban na ‘yansanda ya ce ba zai kara lamuntar kai hare-hare wa ‘yansanda a bakin aiki ba.
IGP din ya umarci dukkanin shalkwata-shalkwata da rassan hukumar da su farka kana su dauki matakan da suka dace wajen kama masu irin wannan dabi’ar tare da tabbatar an gurfanar da su a gaban kotu domin fuskantar shari’a daidai da laifukansu.
Kakakin ya ce shugaban ‘yansandan ya jaddada aniyarsa ta kare rayuka da lafiyar jami’ansa tare da tabbatar musu da yanayi aiki cikin walwala da jin dadi domin sauke nauyin da ke kawukansu a kowani lokaci.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp