ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Masana Sun Bayyana Ingancin TELA Maize Ga Rayuwar Al’umma

by Rabi'u Ali Indabawa
1 year ago
Masana

A yayin da ake ci gaba da nuna shakku game da binciken da aka yi na gano kwayar halittar (GMOs) da aka sabunta, wata tawaga ta kwararrun malamai da masana kimiyya daga Cibiyar Binciken Aikin Noma ta (IAR), Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, ta bayyana cewa kwayar ba ta da wata matsala ga al’umma.

Furofesoshin sun bayyana cewa wannan kwayar halitta suna (TELA maize), a turance, wadda suka samar ta hanyar bincke, ba ta cutarwa, inda suka kara da cewa fasaha da kirkire-kirkire su ne mafita mafi kyau idan har ana so a magance karancin abinci.

  • An Umarci Ƙananan Hukumomi Da Su Ba Da Gudunmawar Miliyan 670 Domin Siyo Motoci Ga Masarautar Kano
  • Masarautar Bauchi Ta Sauya Shawara: Za A Yi Hawan Daushe

Sai dai kuma farfesoshi sun tabbatar wa ‘yan Nijeriya kariya da fa’idar masara ta wannan nau’in amfanin gona da aka gyara ta hanyar da ta dace domin tunkarar kalubalen aikin gona wato, TELA Maize

ADVERTISEMENT

Manufar samar da wannan TELA ita ce, tana jure fari tare da kuma farmakin kwarin da addabar amfanin gona.

A wata ziyarar ban girma da ta kai shalkwatar kamfanin LEADERSHIP a Abuja, tawagar karkashin jagorancin wakilin shugaban IAR, Farfesa Lucius Bamaiyi, ta ce ziyarar cibiyar na da nufin kawar da gurbatattun bayanai da kuma bayanan da ba su da tushe game da GMOs, musamman game da masarar TELA mai cike da cece-kuce.

LABARAI MASU NASABA

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

Farfesa Bamaiyi ya bayyana ainihin aikin IAR a matsayin habaka nau’ikan dimbin amfanin gona da kuma jure fari wadanda suka dace da bukatun noma a Nijeriya.

Ya bayyana masarar TELA a matsayin wata sabon salo da kirkira ta zamani a kimiyyance domin magance matsalolin da ake ci gaba da addabar amfanin gona, kamar kwari da canjin yanayi.

Aikin “Masarar TELA bai takaita kan inganci da wadatar abinci ba, har ma tana ba da kariya ga rayuwar manoma, da inganta noman da kuma magance ainihin illar da tsutsotsi ke haifarwa, gami da juriya a yayin fari,” in ji shi.

Shi ma da yake jawabi a yayin ziyarar, Farfesa Muyideen Oyekunle, wani masani a fannin tsirrai kuma daya daga cikin jagorori masu bincike kan aikin masarar Tela, ya gano yadda akre bunkasa wannan noma tun a farkon shekarar 2019.

Ya jaddada cewa bayan shekaru masana kimiyya, tantance hadarin, da kuma bin ka’ida, sun tabbatar da cewa masara ba ta da wata illa ga dan’Adam da muhalli.

“Bincikenmu ya tabbatar da cikakkiyar hujja akan haka, kuma ya yi daidai da ka’idojin aminci na duniya. Abubuwan da ke tattare da GMOs ba a ma fara bayyana shi ba.

TELA maize ta samu duk wani bincike da ya dace a ce an yi domin kare lafiyar halittu, kuma muna da yakinin cewa ba ta da wata illa ga lafiyar dan’Adam,” in ji Farfesa Oyekunle.

Wata kwararriya daga Cibiyar, Farfesa Memuma Abdulmalik, wadda ta tabbatar da hakan, ta bayyana cewa an samar da TELA maide ne domin noman masara mai inganci tare da kawar da duk wani nau’i na kwari da kuma fari.

A cewarta, wadannan gyare-gyaren ba sa canza tsarin abinci mai gina jiki ko amincin amfanin gona.

“Manufar inganta kwayoyin halittar TELA maize ita ce kare amfanin gona daga kamuwa da tsutsotsi dake addabai tsirrai da kuma sanya jurewar fari. Bayan wannan babu abu abu mai cutarwa ga masarar ko kuma haifar da wani hadari ga muhalli,” in ji ta.

A nasa bangaren, Farfesa Shehu Ado ya bayyana cewa daga cikin amfanin masarar TELA maize, yana matukar rage bukatar magungunan kashe kwari, wadanda galibi ke haifar da illa ga lafiya da muhalli fiye da amfanin gona.

Ya kara da cewa, “Ta hanyar rage dogaro ga magungunan noma masu cutarwa, masara ta TELA maize na ba da gudummawa ga tsarin noma mai dorewa kuma wanda ya dace da muhalli,” in ji shi.

Masanan sun kuma yi nuni da cewa, bayanai marasa tushe da ake yadawa game da GMOs ya haifar da koma-baya ga sabbin ayyukan noma da za su ceto rayuka a Nijeriya. Sun bukaci kafafen yada labarai da su rika gaggauta yada sahihan bayanai masu alaka da kimiyya.

Masarar TELA maize, wadda aka samar a karkashin gidauniyar TELA ta fasahar noma ta Afrika wato (AATF) tare da hadin gwiwar IAR da sauran masu ruwa da tsaki, na ci gaba da gudanar da gwaje-gwajen gonaki da yawa, kuma a halin yanzu an amince da noman a yankuna da dama a Nijeriya.

Yayin da ake ci gaba da muhawarar jama’a game da kayan amfanin gonar, kungiyar IAR ta sake jaddada aniyarta ta tabbatar da gaskiya, aminci, da samar da mafita wadanda ke karfafa wa manoma domin tabbatar da an samar da isasshen abinci a kasa.

Nijeriya na iya tanadin Naira Biliyan 900 duk shekara ta hanyar TELA Maize – IAR

Cibiyar Binciken Aikin Noma ta Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ta bayyana cewa Nijeriya za ta iya yin tanadin sama da Naira biliyan 900 a duk shekara ta hanyar amfani da irin masarar TELA da aka samar ta hanyar kwayoyin halitta.

A cewar cibiyar, daga cikin irin gudunmawar da masarar TELA za ta bayar, akwai rage dogaro da magungunan kashe kwari da ake shigowa da su daga waje da ake amfani da su don yakar kwari masu lalata amfani kamar farin Dan go.

Babban daraktan hukumar ta IAR, Farfesa Ado Adamu Yusuf, ya bayyana irin gagarumar fa’idar da masara ta TELA ke samarwa a fannin tattalin arziki da noma, sannan ya jaddada bukatar a gaggauta gyara kura-kuran da jama’a ke yi game da amfanin gonakin fasahar kere-kere.

A cewarsa, Nijeriya na kashe sama da Naira biliyan 900 (kimanin Dalar Amurka miliyan 600) a duk shekara wajen shigo da magungunan kashe kwari don magance kwarin masara kamar farin Dan go, ban da kudin aikace-aikace.

Ya lura cewa bullo da masarar TELA mai jure kwari da jure fari (SAMMAZ 72T zuwa 75T) zai rage kashe kudaden da ake yi sosai, tare da habaka amfanin gona, da kuma adana ajiyar waje.

Muhimman fa’idodin masarar TELA da aka bayyana a yayin ziyarar sun haɗa da: jurewar kwari, jure fari, ƙara yawan amfanin gona da kuma samar da abinci.

Masana
Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ƙungiya Ta Gudanar Da Zaɓen Sabbin Shugabanninta A Abuja
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Yadda Tinubu Ya Kashe Naira Biliyan 37.64 A Tafiye-tafiye
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ta’addaci: Mutum 14,500 Sun Bace A Arewa Maso Gabas

MASU ALAKA

Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila
Manyan Labarai

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

September 9, 2026
ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto
Labarai

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja
Labarai

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Next Post
Kotu Ta Ɗage Shari’ar Yahaya Bello Zuwa 26 Ga Yuni Don Yanke Hukunci

Kotu Ta Ɗage Shari'ar Yahaya Bello Zuwa 26 Ga Yuni Don Yanke Hukunci

LABARAI MASU NASABA

Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

September 9, 2026
ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.