Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ce alakar Sin da Rasha ta zama misali na kyakkyawar dangantaka tsakanin manyan kasashe, wadda ke kunshe da ingantaccen yanayin kawance na makwafta, da cikakken salon tafiya tare bisa manyan tsare-tsare, da hadin gwiwar cimma moriyar juna. Shugaba Xi ya bayyana hakan ne a Talatar nan, yayin zantawarsa da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin a birnin Beijing.
A nasa tsokacin kuwa, shugaba Putin ya ce shawarar da shugaba Xi ya gabatar game da tsarin shugabancin duniya ta zo a lokacin da ake matukar bukatarta, kuma wajibi ne a yi aiki da ita, kana za ta taka muhimmiyar rawa wajen magance gibin dake akwai a tsarin shugabancin duniya.
Ya ce a nata bangare, Rasha a shirye take ta ci gaba da raya hadin gwiwa da bangaren Sin bisa manyan tsare-tsare, da wanzar da musaya bisa matsayin koli, da karfafa hadin gwiwar zahiri da Sin a mabanbantan sassa, da yayata ci gaban alakar sassan biyu bisa matsayin koli.
Sassan biyu dai sun sanya hannu kan yarjeniyoyin hadin gwiwa sama da 20 a bangarorin da suka hada da na makamashi, da sufurin sama, da AI, da noma, da lura da kare bazuwar cututtuka. Sauran sun hada da fannin kiwon lafiya, da binciken kimiyya, da ilimi da watsa labarai. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp